Advert
Home Sashen Hausa Labarin wata Unguwa a jihar Katsina

Labarin wata Unguwa a jihar Katsina

LABARIN WATA UNGUWA A JIHAR KATSINA.

Daga Engr. Abu Aminu

Unguwar …tana da kimanin gidaje 300. Kamar kowacce unguwa suna da Social Classes, Masu hali, middle Class da kuma Raw Materials (mu talakkawa).

Masu halin unguwar suna kai yayansu wata makaranta mai tsada amma nesa Wanda hakan yana kawo zullumi na tsaro. Middle class Nada makarantun kudi cikin unguwa, wadanda basu da standard basu da tarbiyya, saidai anasamun Result mai kyau. Ko ya ake suna cin SSCE duk da cewa malamansu Corpers ne da drop outs? Wannan bansani ba.

Dangi Kuwa(Raw materials) na unguwa Kuma basu da option sai su tura yaransu magarantar gwamnati ta cikin unguwa. A wannan makaranta akwai professional malamai, saidai basu zuwa kuma suna aikin yanda suke so, babu monitoring daga gwamnati ba supervision. Wanda hakan kesa baa cin jarabawa, babu tarbiya, don babu kula babu ko kujerar staff room bare ta aji.

A wannan yanayin ne aka samu wasu zarata suka kira taron ilimi na unguwa. A wurin taron aka yanke shawara Kamar haka:
1-Zaa hada kai ayi tafiya duka tare da fahimta.
2-Maimakon kudin makaranta #15000 da suke biya ma yara a wadancan makarantun kudin, yanzu duk mai son shiga shirin zai bada #10000 a term. Saboda haka ‘kowa’ ya maido danshi makarantar gwamnati ta cikin unguwa.
Wannan #10000 per child per term daga iyaye 100 zaa biyata ne first term, sauran Terms zaa biya #3000 ne.
Ga abinda akayi da kudin.
30%- gyaran makaranta.
30%- Zaaba malaman makarantar allowance don suyi aiki dagaske.
20%-Kayan aiki.
10%-Scholarship na marayu
10%-A aje maganin takwana.

Yanzu dai halin da ake ciki, angyara makaranta daidai gwargwado, azuzuwa nada taga da kofofi da rufi. Don matasan unguwa masu Sana’a welder aka ba aikin gyaran.
2-Malamai nata Rushing ayi masu Transfer zuwa makarantar wannna unguwa, duk da cewa aiki ya qaru, tunda anbude karatun marece don a rage cunkuso.
3- Committee da aka Nada na monitoring da supervision suna aikin su da himma. Daman retired maaikatan gwamnatine da suka San darajar ilimi.
4-Yara an hadu babu bambanci.
5-Babu yaran da baizuwa makarantar saboda Rishin kudi.
6-Saboda wannan qoqarin na yan wannnn unguwa, yanzu duk abinda gwamnati zatayi ana basu special recognition.
7-Yan unguwa ke gadin makarantar, don sun San idan aka saci kofa ko taga, kudinsu ne zasu sa su gyara.
8-Yara na samun guidance and counselling akai akai.
9-Anyi hadin gwiwa da masu Sana’a, India ake koya ma yara masu Interest sanaoin dogaro da kai.
10-Saboda wannan tsarin yanzu Unguwar akwai qarancin masu shayeshaye.
11-Saboda wannan hadin kan, yanzu anrage samun mutuwar aure a Unguwar. Don ana amfani da dattijan unguwa wurin settling issues kafin su hauhawa.

Wannan unguwa bawata unguwa bace, saidai unguwarku CE. Idan aka hada kai, zaa iya yin haka.
Yakamata mu sani, lokacin jiran gwamnati tayi mana komai ya wuce.
Mutashi tsaye mu hada kai mu taimaki kanmu.
Ka/ki fara shawara da makwabta, masu unguwa don cimma wannan buri.
Allah Raya jihar katsina.

Shawarata ta 997

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

VICTIMS OF KIDNAPPINGS IN BATSARI REGAIN FREEDOM AFTER 66 DAYS IN CAPTIVITY.

From Misbahu Batsari. Some of the victims of kidnappings were this Friday 23-07-2021 release from captivity in Batsari after spending 66 days in the hands...

Just In: Plane Crash Lands In Kwara, Passengers Evacuated

Many passengers, including some highly placed Nigerians, narrowly escaped death after an aircraft belonging to one of the major airlines crashed upon landing in...

Yar’Adua: I’ll Resist Attempt to Impose Guber Candidate on Katsina Citizens

Francis Sardauna in Katsina A chieftain of the ruling All Progressives Congress (APC) in Katsina State, Senator Abubakar Sadiq Yar’Adua, yesterday vowed to resist any...

Mansurah Isah Ta Yi Allah-ya-isa Kan Mutuwar Auren Ta

DAGA IRO MAMMAN “Allah ka saka min. Allah abin da su ke min ka yi musu, ka yi wa yaran su, iyayen su, ‘yan’uwan su....
%d bloggers like this: