Advert
Home Sashen Hausa LABARI| Wasu rahotanni na nuni da cewa akwai yiwuwar Gwamna El-Rufai na...

LABARI| Wasu rahotanni na nuni da cewa akwai yiwuwar Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya nada Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.  Dama ta ta6a rike mukamin a wa’adin

Dama ta ta6a rike mukamin a wa’adin mulkin farko na El-Rufai daga 2015 zuwa watan Yulin 2016. Kafin daga bisani shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ta mukamin shugabancin Hukumar Tasoshin Ruwa ta Nijeriya (NPA) a 2016.

An kuma sabunta mata mukamin a wa’adin mulki na biyu na shugaba Buhari. Sai dai a watan Mayun 2021 shugaban kasar ya amince da cire ta daga mukamin bisa wadansu zarge-zarge ciki harda na cin amanar ofis din.

El-Rufai zai ba ta mukamin na yanzu ne biyo bayan matakin sauyawa Muhammad Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Dattijo mukami daga shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin zuwa Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi mukamin da shima ya ta6a rikewa a baya.

Sauya masa mukamin ya zo ne makonni biyu da Dattijo ya gabatar da Muhammadu Sanusi II a matsayin ‘Tsohon Sarkin Kano’ a taron KADINVEST 6.0, inda nan take Muhammadu Sanusi II ya mayar masa martani da cewa; shima ‘Tsohon Shugaban Ma’aikatan fadar gwamnatin jihar’ ne wanda ya ce zai fahimci hakan a gaba duk da a lokacin yana rike da mukamin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Gwamnatin Katsina ta Amince da gina hanyar ƙarƙashin ƙasa (Underpass Road) a cikin Birnin katsina…

  A zamanta na yau Laraba 20 ga watan Oktoba 2021, Majalisar zartaswa ta jiha karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta amince da gina...

PHOTOS: Buhari Receives Turkish President Erdogan, Wife in Abuja

The President, Major General Muhammadu Buhari (retd.), has received the Turkish President, Recep Tayyip Erdogan and his wife, Emine at the State House in...

Gwamnatin Kaduna ta ce an kashe mutum 343 cikin wata uku a jihar

Daga: Comrade Musa Garba Augie. Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 343 sakamakon ayyukan 'yan fashin daji da sauran tashe-tashen hankali cikin wata...

Shekarau ba uban Gidana bane A siyasa ,,,, Abokin Siyasa Tane Kawai ,, Cewar Musa Iliyasu Kwankwaso…

Ni Bana Adawar Cikin Gida Amma Duk layin Dayake Na Gaskiya Shinake bi Kuma Layina Shine Abdullahi Abbas,,, Cewar Musa iliyasu Kwankwaso, Saidai Yayi tsokaci...

RIKICI TSAKANIN MAHDI SHEHU DA GIDAN REDIYON VISION FM KADUNA!

  Musa Ibrahim daga Kaduna @Katsina City News Wani rikici ya barke tsakanin malam mahadi shehu shugaban rukunin kamfanonin dialogue da kuma gidan rediyon vision FM...
%d bloggers like this: