Labari Da Duminsa: Coci Ya Ruguzo Kan Masu Bauta Ana Cikin Ibada A Jihar Taraba

Rahoton Daily News Hausa

Ginin coci ya ruguje a jihar Taraba, inda ya kashe mutane biyu tare da jikkata masu ibada da dama.

Rahoton da muka samu ya ce Cocin na Holy Ghost Church, yana cikin garin Chanchanji ta karamar hukumar Takum ta jihar.

Shugaban karamar hukumar Takum, Shiban Tikari ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Asabar da gidan talabijin na Channels.

Wadanda abin ya rutsa da su – Demenege James da Mwueze Terzunwe – an ce suna ibada a cocin da ke kauyen Peva kafin ginin ya tsage.

Ya bayyana cewa wadanda suka jikkata suna karbar magani a cibiyar kula kiwon lafiya ta makakin farko a yankin.

DAILY NEWS HAUSA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here