Jami’an hukumar hana fasa ƙwabri ta Nijeriya Kwastan, sun kai samame a kamfanin sayar da motoci na Maslaha, mallakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Shitu S Shitu, inda suka tafi da kimanin motoci 20.

Jami’an sun kai samamen ne da misalin ƙarfe 1:30nd na dare, wayewar safiyar Talatar nan.

Da yake yi wa ƴanjarida bayani a safiyar yau Talata shugaban kamfanin Alhaji Shitu Maslaha, wanda ya ce jami’an na Kwastan sun ɓalla ƙyauren kamfanin sun shiga, duk da akwai makullai a hannunsu, ya yi mamakin yadda suka tafi da wasu motoci duk da a cewarsa suna da Kwastan Duti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here