Kwastam ta kama ƙwanson dabbar pangolin na kusan biliyan ɗaya a Legas

Hukumar kwastam a Najeriya ta kama ƙwanson dabbar pangolin da ake kira ɗan kunya ko kuma batoyi da kuɗinsa ya kusan naira biliyan ɗaya.

Kwantirola kwastam a Apapa, Muhammad Abba Kura, ya ce an kama tan dubu 850,000 na ƙwanson a cikin wata maƙareriyar kwantaina mai tsawon taku ashirin da ke kan hanyar zuwa birnin Haipong na ƙasar Viatenam.

Kwantirola Muhammad Abba Kura ya ce bayan an yi bincike sosai, hedikwatar hukumar za ta dauki matakin da suka dace daidai da dokokin kare muhalli da dabbobi, musanman wadanda ke fuskantar barazanar ƙarewa a duniya.

LAGOS

Yarjejeniyar kasuwancin ta ƙasa da ƙasa kan dabbobin da ke fuskantar barazanar gushewa daga doron duniya ta 1973, ta nuna cewa hukumomin kwastam a faɗin duniya suna cikin sahun hukumomi da ke kare namun daji domin hana cinikinsu ta haramtacciyar hanya.

Masana dabbar ɗan kunya ko batoyi wato Pangolin na cewa wasu shu’uman ko hatsabiban mutane na amfani da bawon dabbar domin hada silke da ke hana harsashin bindiga ratsa jikinsu.

Ana da yaƙini cewa sassan dabbar pangolin su ne mafi yawan wadanda akan yi fataucinsu a duniya, baya ga fataucin bil’adama wadanda ya kai kusan kashi 20 cikin 100 na duk cinikin haramtattun sassan namun daji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here