AN RANTSAR DA KWAMITIN DAZAI BINCIKI MUSABBABIN GOBARAR DATA ABKU A MAJALISAR DOKOKI TA JIHAR KATSINA RANAR 21/04/2021.

A ranar Talata 27/04/2021 kakakin majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Rt. Hon. Tasi’u Musa Maigari Zango ya rantsar da Kwamitin dazai binciki musabbabin gobarar data faru a zauren majalisar Dokokin.

Aikin Kwamitin, na farko ya binciki musabbabin abinda ya haddasa Gobarar, da yadda za’a dauki matakai na kare abkuwar ta a gaba, na biyu ya tantance irin asarar da gobarar ta haddasa da kuma lissafin yadda za’a sake maida ginin zauren majalisar ya dawo yadda yake don cigaba da gudanar da aikin majalisar yadda yakamata.

Wadanda aka rantsar sun hada da:

Hon. Abubakar Suleiman Abukur (House Leader), shugaba
Hon. Lawal H. Yaro Away daga Shiyyar Funtua mataimakin shugaba
Hon. Salisu Hamza Rimaye daga Shiyyar Daura Memba
Hon. Aminu A. Garba daga Shiyyar Katsina ta Tsakiya, Memba
Hon. Abubakar M. Total Memba
Wakili daga hukumar Yan Sanda, Memba
Wakili daga hukumar kare fararen hula, Memba
Wakili daga hukumar yan sandan farin kaya, Memba
Dogarin Majalisa, Memba
Wakili daga hukumar kashe gobara, Memba
Mai kula da gyare, gyare da ajiya na Majalisar, Memba
“HOD (LEGAL)” , Memba
“HOD (Admin”) , Memba
Wakili daga ma’aikatar lafiya ta Jihar Katsina, Memba
Mataimakin Akawun majalisar, Sakatare.

Bayan Rantsar da Babban Kwamitin nan take ya kirkiro da kananan Kwamiti guda biyu:

Karamin Kwamitin na farko, aikin shi zai binciki abinda ya haddasa gobarar, ya kuma binciki yadda yanayin wurin yake kafin abkuwar gobarar, Membobin Kwamitin sun hada da:

Hon. Lawal H. Yaro shine zai jagoranci aikin Kwamitin, sauran sun hada, Hon. Salisu Hamza Rimaye, Dukkan Jami’an tsaron dake cikin Kwamitin, “HOD (Legal Services”) DLM Sakatare.

Karamin Kwamitin na biyu, aikin shi zai binciki irin illar da gobarar tayi ma ginin zauren majalisar, ya kuma yi kiyasin abinda zai sake gina zauren majalisar, Membobin Kwamitin sun hada da:

Hon. Abubakar M. Total shine zai jagoranci aikin Kwamitin, sauran yan Kwamitin sun hada da, Hon. Aminu A. Garba, Wakili daga ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Jihar Katsina, “HOD (Admin and supplies”) , Mai kula da ajiya da gyare, gyare na Majalisar, Malam Falalu Ahmad Sakatare.

Kananan Kwamitocin zasu gabatar da aikin binciken da suka gudanar ga Babban Kwamitin cikin sati daya, Babban Kwamitin zai gabatar da Rahoton binciken shi ga majalisar cikin sati biyu da rantsar dashi.

A lokacin rantsar da Kwamitin binciken, shugaban majalisar Hon. Tasi’u Musa Maigari Zango ya jawo hankalin yan Kwamitin da suji tsoron Allah wajen gudanar da aikinsu, Kuma su tabbatar sun bayyana gaskiyar akan abinda ya faru bisa adalci.

Rahoto

Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
27, April 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here