Advert
Home Sashen Hausa Kwamitin Bincike ya tabbatar da Cewa DCP Abba Kyari ya karbi rashawa...

Kwamitin Bincike ya tabbatar da Cewa DCP Abba Kyari ya karbi rashawa daga ‘dan damfara Hushpuppi.

Yanzu nake Samun labari daga Jaridar Punch cewa Kwamitin Bincike na Musamman kan badakalar Abba Kyari ya mika rahotonsa ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba alkali, bayan makonni biyu da aka umarce shi da ya binciki tsohon Shugaban rundunar IRT kuma Mataimakin Kwamishinan’ Yan sanda, Abba Kyari. Kwamitin na mutum hudu karkashin jagorancin Mataimakin Sufeto -Janar na ‘yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na rundunar, Joseph Egbunike, ya mika sakamakon binciken ga IG ranar Litinin 16 ga watan Agusta. A baya mun ji rahoto cewa, hukumar FBI ta kasar Amurka ta zargi Abba Kyari da hannu cikin wata damfara da Abbas Ramon (Hushpuppi) ya yi kan wani dan kasuwar Qatar, Punch ta ruwaito.

Yo daman aina fa’di maku Abba Kyari ya Gama Samun Matsala duba da yadda Hujjoji suka nuna Suka kuma a bayyana a zahiri Amma Mutane mun fa’di maku kunce Rashin kishin Arewa ne, ni bazan iya Kare Arewa a Kan karyaba…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: