Akalla gawarwakin mutum 18 aka tsamo daga wani kogi a karamar hukumar Mai’adua ta Jihar Katsina bayan da kwalekwalen da suke ciki ya nutse da su.

Jaridar Daily Trust wadda ta wallafa labarin, ta ce wani mazaunin yankin mai suna Lawal Sakatare ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya ce mutum 24 ne ke cikin kwalekwalen wadanda suke tafi yawon sallah.

Mallam Lawal ya ce mutum 18 da ke cikinsu sun halaka, inda ya ce yawancinsu kananan yara ne:

“Mutum 14 daga kauyen Tsabu suke, inda mutum hudu kuma mutanen kauyen Dogon Hawa ne. An binne 15 cikin mutum 18 din a Mai’adua a ranar Alhamis din nan, sai dai har yanzu ba a ga mutum shida ba.”

Har zuwa lokacin da aka hada wannan rhoton, ‘yan sanda a Jihar Katsina ba su ce uffan ba kan lamarin, amma mazauna yankin sun ce sun ci gaba da aikin nemo wadanda ba a ga gawarwakin nasu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here