Kwalejin Ilimin Lafiya Ta Khuddam Katsina Ta Yi Bikin Rantsar Da Sabbin Dalibai.

Kwalejin Ilimin kimiyyar lafiya ta Khuddam da ke Katsina, ‘Khuddam College Of Health Technolgy’ a turance, ta yi bikin rantsar da sabbin daliban zangon karatun shekarar 2020/2021 a Makarantar.

Taron rantsarwar wanda yake a karo na biyu, an gudanar da shi ne a ranar Lahadin nan a dakin taro na Makarantar da ke a AB Sanda Plaza, daura da Makabartar Danmarna, kan Titin Kofar Kwaya, Katsina.

Da yake jawabi a taron da harshen turanci, uban taron, Alhaji Husaini Dambo ya ja hankalin sabbin daliban wajen yin karatu tukuru tare da daratta Malamansu don samun albarkar karatun, musamman irin wannan karatu na harkar lafiya mai bukatar jajircewa da sadaukarwa. Ya kuma gargadi daliban kan dogara ko sakankancewa da aikin gwamnati, inda ya ce samun aikin gwamnati ba tabbas ba ne yanzu, don haka tun da wuri su nemi sana’o’i su kara da su bayan wannan da suke yi, kodayake da wuya mutum ya karanci ilimin harkar lafiya ya kuma zauna hannu rabbana.

Shi ma a nashi jabawabin a cikin wata Kasida da ya gabatar a taron, dan siyasa kuma Malami, Dakta Muttaka Rabe Darma, a wani salo ya ja hankalin daliba kan yadda za su yi amfani da abin da suka koya don ya amfane su ya kuma amfani sauran al’umma.

A lokacin taron rantsar da daliban, an gudanar da Jawabai da kasidu wanda Malamai da Manyan mutane masu fada a ji suka gabatar. An kuma gabatar da taken Kasa (National Anthem), da bayar da lambar yabo ga wasu zakakuran daliban Makarantar, da yin Hotunan tarihi, daga bisani kuma aka sakarwa Sipiku sautin Kida inda aka cashe ta hanyar rausayawa.

Bikin rantsarwar dai ya samu halartar Iyaye, Malamai da Dalibai, ‘yan Siyasa, ‘yan jaridu da sauransu. Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron, akwai; shugaban kungiyar nan ta maido da abubuwa yadda suke Malam Sabo Musa, Dan Majalissar jiha mai wakiltar karamar hukumar Katsina Honarabul Abu Ali Albaba, shugaban PLBC Dakta Muttaka Rabe Darma, da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here