Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yayi kira ga magoya bayan jam’iyyar APC na jihar Kano, akan cewa suyi hakuri su rungumi zaman lafiya da bin doka da oda, musamman akan hukuncin da wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yanke a wannan rana, wacce ta sake tabbatar da zaben shugabancin APC ta tsagin tsohon gwamnan Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau.

Majiyar Nasara Radio (Amanar Talaka) ta rawaito cewa, bayanin hakan ya fito ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar Kano, kwamared Muhammad Garba, wacce gwamna Ganduje yace wannan lamari ne wanda ya shafi jam’iyyarsu, saboda haka zasu bibiyi yadda abin ya kasance domin sanin matakin da za’a dauka a gaba.

Kazalika gwamna Ganduje ya bukaci jami’an tsaro da kada suyi sanya wajen tabbatar da bin doka, domin gwamnati ba zata lamunci duk wani nau’in laifi ko tada hargitsi a sassan jihar Kano ba, ta sigar siyasa ko wani fanni. Daga nan gwamna ya godewa masu ruwa da tsaki da dukkan mambobin jam’iyyar APC, bisa goyon baya da suke bayarwa.

Nasara Radio 98.5 FM
17/12/2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here