“Kuyi haƙuri ku janye Ƙara na amsa buƙatar kuta tsayawa takara.” Salisu Isansi ga Ƙungiyoyin da suka kaishi Kotu.

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

 

A cikin gaggawa Hon. Salisu Iro Isansi, Ɗan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar Katsina, ya kira taron ‘yan Jaridu domin tabbatar wa ƙungiyoyin da suka makashi Kotu cewa su maida wuƙar, sukai zuciya nesa ya amsa kira, kuma yana roƙo da su janye ƙarar da suka shigar.

Salisu yace: “Abinda yasa kukaga na ƙi sayen Fom ɗin takara, saboda dalilai guda biyu, na farko’ ida aiyyukan da ke gaban na majalisa zuwa ga talakawa da suka zama wajibi, na biyu Azumi da ya ratsa. watan Ibada wanda yana da kyau mu tunkari watan da ibada domin neman Rahamar Ubangiji da samun dace, sana kuma inaga har yanzu bamu makara ba duba da lokacin da Uwar Jam’iyya ta bayar bai ƙare ba. Don haka na amsa zan fito takara.” Inji Salisu.

Salisu ya bayyana wasu muhimman Ayyuka da ya gabatar a mazaɓarsa ta Katsina irn su gina Titina makaranta da ƙara gina wasu azuzuwa a cikin wasu makarantu, da samar da ɗakunan karatu na zamani a buɗaɗɗiyar jami’a da wata a cikin tsohon ginin Labirari ta cikin birnin Katsina. Sana Isansi ya taɓo wasu ƙudirori da ya kai a gaban Majalisa waɗanda wasu an gabatar da su wasu kuma ana kan karatunsu kuma zasu amfani duka Arewacin Najeriya bama mazaɓar sa ba.

Hon. Isansi ya ƙara da cewa, “Babban abinda ke maida mu baya a ƙaramar hukumar Katsina, shine rashin tsayawa don gina wakilci, ma’ana shi wakili a majalisa kamar Iccen Mangoro ne, duk sanda ka shuka zaka dunga kula da shi, da bashi ruwa sai ya girma ya kusa isa ka amfana da shi, sai kuma ka datse shi, ka dasa wani, idan har ana haka babu ranar da za’a moreshi.” Inji Honorabul

Yace, a cikin shekarun da basu wuce uku ba, ya je majalisa kuma har yanzu cikin karatun majalisar yake, kamar yaro ne yaje aji ɗaya yaje biyu, yaje uku, to idan har ana so aga kwazonbsa abarshi yagama makaranta domin aga da wane sakamako zai fita? “Yanzu muka shiga majalisa muke karatu, amma mun gabatar da wasu muhimman ayyuka da a iya sanina wannan majalisar tana ɗaya daga cikin waɗanda suka gabatar da muhimman ayyuka, to ina ga am bamu dama munyi na farko munyi na biyu har zuwa na uku, a lokacin mun goge munsan ciki da bai-bai ɗin ta, mun samu jagorancin wasu kwamitoci da ko don su, zaka samarwa ƙaramar Hukumar ka gagarumin ci gaba…?” Ya tambaya.

Salisu ya roƙi Al’umar Katsina da su ƙara bashi dama, saboda ƙara samar da ci gaba, idan kuwa ba haka ba, kullum ƙaramar hukumar Katsina zatai ta dashe kafin amfanin yazo kuma an cire dashen an sake dasa wani, babu ranar da za’a mori abinda aka dasa. Yace.

Karshe Salisu ya tabbatar da zai sayi Fom domin tunkarar zagaye na biyu a majalisa idan Allah ya nufa.

An gudanar da taron a 3AS gidan taro da cin abinci dake kan Titin Ring Road, Kabukawa Commacial Estate Daura da gidajen Faitma Shema, a garin Katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here