A Matsayin ka na Ɗan Najeriya yaya kaji da wannan kiran na Shugaba Buhari…

Buhari Ya Roki Ƴan Bindiga Su Sako Sauran Ɗaliban Jami’ar Greenfield ta Kaduna.

Shugaba Muhammadu Buhari ya roƙi ƴan bindigar da su sako sauran daliban Jami’ar Greenfield ta Kaduna da har yanzu ke tsare a hannun su kuma sukayi barazanar cewa zasu kashe su ranar Talatar da ta gabata idan ba’a basu kudin Fansa ba.

Kazalika kuma yayi roƙon da su sako duk wani da aka yi garkuwa da shi a fadin kasar nan.

Wannan roko na cikin wata sanarwar taya ɗaliban Babbar Kwalejin kula da Gandun Daji dake Kaduna da aka kubutar da su daga hannun ‘yan bindiga, bayan sun shafe sama da kwanaki 50 a tsare.

Cikin bayanin da Kakakin Yad’a Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, Buhari ya taya ɗaliban na ‘Federal College of Foresty Mechanizarion, Afaka su 27 murnar kubuta daga hannun ‘yan bindiga.

Ya kuma taya iyayen su da gwamnatin jihar Kaduna murnar ganin karshen wannan Ibtila’in

“Mu na kuma godiya ga dukkan wadanda su ka sa hannu su ka taimaka wajen kawo karshen wannan matsala, musamman jami’an tsaro, jami’an Ma’aikatar Muhalli da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna. Kuma mu na godiya ga ‘yan Najeriya dangane da addu’o’in da su ka rika yi.”

Sai dai Buhari ya nuna damuwa kan masu amfani da siyasa su na kara rura wutar matsalar tsaro a kasar nan.

Sannan kuma ya jaddada ƙoƙarin sa wajen tabbatar da cewa ƴan Najeriya sun riƙa samun walwala da zirga-zirgar zuwa ko’ina a fadin ƙasar nan, ba tare da tsoron masu garkuwa ko ‘ƴan bindiga ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here