Kungiyoyin Al’uma daga yankunan kananan hukumomin jihar Katsina sun tarbi Sanata Yar’Adua a wajen bikin bada tutar APC…

Dubban Al’uma kungiyoyi daga ko ina a fadin jihar ta Katsina suka tarbi Sanata Sadiq Yar’Adua kuma mai neman takarar Gwamnan jihar Katsina, a wajen bikin bada tutar jam’iyyar APC ga ‘yan takarar shugabanin kananan hukumomi a 34 na jihar Katsina da ya gudana a garin Kankia.

“Mun fito ne domin nuna goyon bayan mu ga wannan dan takara da muka san Amfanin zabar mutanen kirki domin sa, saboda ta dalilin sa mukasan aikin cigaba da raya kasa da al’umma, a lokacin yana sanata.” Inji wani daga cikin magoya bayan Sanatan.

Sanata Abubakar Sadiq Yar’Adua ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Katsina ne, bayan kiraye-kirayen Al’uma a fadin jihar da cewa shine ya cancanta da y zama Gwamna ba don komi ba sai don kwarewar sa a jagoranci da mu’amala da mutane.

Ko a watan da ya shude kungiyoyin tsaffin ma’aikata a fadin jihar Katsina sun shirya wata tattaunawa ta musamman a yankunan Daura Funtua da Katsina domin nuna goyon bayan su akan takarar ta Sanata, a cewar su, shine mutumin da yasan hakkokin su, kuma suna fatan zai share masu hawayen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here