Kungiyar ta’addanci ta Ansaru sun yi rabon kayan Azumi a ƙauyukan Jihohin Katsina, Zamfara da kuma Kaduna. Ƙauyukan sun hada da Kwasa-kwasa, Kuyallo, Shado, Gwandu, Farin Batu, Layin Ɗan Auta, Kwanar Adua, Jabi, Saminaka, Nacibi, Kwadaga, da kuma Shado.

Wani manomi ya sheda cewa yan kungiyar sun ce da shugabannin yan bindiga (Baushe wanda siriki ne ga Dogo Gide da Musa Shado) su bar wannan yankunan da suke nan take. Kungiyar na ta ƙoƙarin samun alaka mai ƙarfi da al’ummomin ƙauyukan da aka ambata a sama.

Suna sanya kayan irin na mutanen Pakistan (Ruwan Toka) tare da riga ta kakin soja.

~Edrees4P

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here