ƘUNGIYAR TSANGAYA TA SHIRYA TARON YIWA JIHAR KATSINA ADDU’A.

Wata ƙungiya mai suna Tsangaya Teaching Association dake jihar katsina, tashirya gagarimin taron yiwa jihar Addu’a akan halin da take ciki.

Ƙungiyar a ƙarkashin jagorancin Shugabanta Sheikh Ibrahim Sheikh Iyal Gafai katsina yayi kira ga membobin ƙungiyar dake faɗin jihar da su gudanar da addu’o,i na musamman akan halin da jihar ta tsinci kanta.

Da muke zantawa dashi bayan gama gangamin addu’ar Malam Ibrahim ya sheda mana cewa sun kira dukkanin wakilan ƙungiyar dake yankunan jihar ta katsina domin fara addu’o,in a kowane Local government talatin da hudu dake jihar.

Munshirya saukar Al’ƙur’ani mai tsarki sauka ɗari a kowane ƙarshen wata na musulinci a duk faɗin jihar nan.

Kuma muna kira ga dukkanin ɓangarorin musulmi cewa yanzu ba lokacin tarurruka bane lokaci ne na addu’o,i ga kowa ‘yanɗarika, Izala ‘Yan shi’a da ‘yan Ƙur’aniyun duka mu maida hankali da addu’a domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Yaƙara da cewa munyanke shawarar nunawa duniya wan’nan addu’o,i da mukayi domin sauran Al’uma suyi koyi, saboda wan’nan matsalar tashafi kowa, ko wane ɓangare kake a Addini, kai harma wanda bashi da addini abinda yafaru a Garin Ƙanƙara yashafe shi, akarshe muna ƙara jaddada kira ga Al’uma da mukoma ga Allah, shine kaɗai zai maganin wan’nan matsala da jihar katsina take ciki.

A garin katsina an shirya taron Addu’ar ne a Masallacin juma’a na FMC dake cikin garin katsina da karfe tara na safiyar Alhamis.

Akwai Video yanda taron addu’ar ya gudana. Sai kuje Shafin mu dake busa yanar gizo.  www.katsinacitynews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here