Advert
Home City News KUNGIYAR NORTHWEST APC SOCIAL MEDIA, TA GUDANAR DA TARON MANEMA LABARAI A...

KUNGIYAR NORTHWEST APC SOCIAL MEDIA, TA GUDANAR DA TARON MANEMA LABARAI A KADUNA KAN MASU ZANGA -ZANGAR KAWAR DA SARS

KUNGIYAR NORTHWEST APC SOCIAL MEDIA, TA GUDANAR DA TARON MANEMA LABARAI A KADUNA KAN MASU ZANGA -ZANGAR KAWAR DA SARS

Qungiyar Matasan Social media na jam’iyyar APC dake yankin Arewa maso Yamma, sun nuna rashin jin dadinsu da yin Allah waddai game da yadda wasu batagarin matasa ke ci gaba da amfani da zanga zangar qyamar jami’an ‘yan sanda masu yaki da ‘yan fashi da makamai, da manyan laiffuka, wanda a turance ake Kira da SARS, ta hanyar yin amfani da wannan dama suna kone konen kayan gwamnati, da kuma sace-sacen dukiyar al’umma, wanda tun a farko ba shi ne maqasudin shirya wannan zanga zangar ba.

Matasan sun bayyana haka ne a yayin da suka Kira wani taron gaggawa na manema labarai a Gidan saukar baqin Gwamnatin Jihar Kebbi dake kaduna, qarqashin jagorancin Shugaban Qungiyar Honarabul Ahmed Rufa’i Gumel, da sauran mambobin qungiyar da suka fito daga daukacin Jihohin Yankin Arewa Maso Yamma, wanda suka hada da, Jihar Kano, kaduna, Kebbi, Jigawa, Zamfara, Sokoto da kuma Jihar katsina.

Matasan sun ci gaba da bayyana cewa, idan dai ba’a manta ba, a makon da ya gaba ne, wasu Matasan Kasar nan suka shirya wani zanga zangar luma nayin Allah waddai da take ‘yancin Dan Adam da suke zargin jami’an ‘yan sanda masu yaki da ‘yan fashi da makamai da manyan laifuka, suke aikatawa a fadin kasar nan, wanda a turance akayi masa lakabi da #Endsars protests.

Sai dai a cewar Qungiyar ta Matasan APC social media, zuwa yanzu abin ya canja salo, domin a cewar su, a halin yanxu wasu ‘yan adawa sun kwace wannan tafiya sun dauki nauyin wasu batagarin matasa domin su shafawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC kashin kaji a idon duniya, ta hanyar bata masa suna da kiran cewa ya gaza ya sauka daga mulki.

Matasan APC social media, sun bayyana cewa, sun gano cewa lalle akwai wasu ‘yan adawa da suka dauki nauyin wadannan matasa, inda suka ingizasu domin yin amfani da zanga zangar suna kona kayan gwamnati, a jihohin Lagos, Kano, Benin, Jos, da kuma sauran wasu sassan jihohin kasar nan, wanda a halin yanzu tuni jihohin sun riga sun sanya dokar ta baci na tsawon awanni 24 domin ganin sun tsare rayuka da kuma dukiyar Al’ummar su.

A cewar Matasan, wuraren da aka konan sun hada da; fasa gidan yari, inda fursunoni suka tsare, sannan sun kona ma’aikatun gwamnati da ofishoshin jami’an rundunar ‘yan sanda, da kuma cinna ma bankuna da wajajen ibadu wuta.

A cewar Qungiyar Matasan, wannan ba karamin abin haushi da takaici ba ne, kuma suna mai yin Allah waddai da duk wasu masu hannu a cikin wannan lamari. Sannan sun shawarci Matasan kasar nan da su ci gaba da baiwa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari goyon baya domin ya cimma manufofinsa na alheri da ya dauko ga Al’ummar kasar nan baki daya. Sannan sun yi kira ga Matasan da su guji yin wani abu da sunan kabilanci ko addini da zai iya jefa Kasar nan cikin hayaniya da tashin hankali. Wanda a cewarsu, babu wata kasa da ta wuce mana Nijeriya.

Matasan sun bayyana cewa, idan ba’a manta ba, da irin hakan yawancin kasashen duniya suka jefa kansu cikin tashin hankali da koma baya, musamman idan akayi la’akari da abin da ya faru a kasashe irin su, Libya, Tunisia, Egypt, Sudan da kuma kasar Syria. A cewar su, ya Kamata mu dauki dimbin darasi a game da hakan.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Alleged Defamation: Gov. Masari demands N10bn, apology from journalists

Gov. Aminu Masari of Katsina State has demanded the payment of N10 billion as damages from Mr. Emmanuel Ogbeche and Mr. Ochaika Ugwu, Chairman...

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina…..

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina..... A ranar Alhamis...

DIRECTOR-GENERAL INAUGURATES NYSC MEGA PRINTING PRESS

NYSC Director-General, Major General Shuaibu lbrahim today inaugurated the NYSC Mega Printing Press in Kaduna. He said the project, which was conceived almost a decade...

Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa, Yarinyar Da Aka Kashe A Kano.

Daga Zaharaddeen Gandu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa 'yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai...