Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 6/12/2021

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya, wato Hunters Council of Nigeria HCN ta karrama Hajiya Umma Dauda Abdullahi, Shugabar Mata Mafarauta ta Najeriya, kuma Mataimakiya ga Shugaban Kungiya ta ƙasa

Kungiyar ta yaba da kokarin da Hajiya Umma Dauda take bayarwa Musamman bangaren tsaron ƙasa, da kuma samar wa Matasa Aikin yi,

An gudanar da taron sake girmama Karamcin na Hajiya Dauda data samu a cikin Birnin Katsina, duba da Yanda Membobin kungiyar na Katsina sukace, dole suyi taro na nuna jin dadi da yanda aka karrama shugabar su, kuma Uwa a wajen su,

taron ya gudana a Ofishin Kungiyar dake Mangal Plaza a kofar Kaura, shekaranjiya asabar 4 ga watan 12 a karkashin jagorancin Shugaban Fityanul’Islam, Alhaji Lawalin Kwashabawa Jibiya, bayan sa Al’barka da godiya ga mahalarta taro, Alhaji Lawal Kwashabawa, yace: “kasancewar su a wajen wannan taro dole ne, duba da Ita wannan jarima, Hajiya Umma itace Mai bada shawara ta Musamman, a cikin Kungiyar Fityanul’Islam ta ƙasa, don haka tanada Muhimmanci garemu”

Taron ya samu baƙuncin Hafiza Maryam Sheikh Tahiru Usman Bauchi, da Farautan Katsina, Alhaji Surajo Mai Asharalle, wakilan jami’an tsaron Roadsafti, Sibil difens, kwastam, gami da baƙi mafarauta, na ciki da wajen Jihar Katsina, Irin su Kano Jigawa Bauchi da sauran su. An nishadantar gami da wasan Farauta, kowa ya nuna bajintar sa, inda aka bawa ƙarfe wuya takobi ta tunkuyi birji.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here