Kungiyar dillalan Albasa daga Arewa ta dakatar da kai Albasa a kudancin Najeriya har sai baba ta gani

Ƴaƴan ƙungiyar dillalan albasa daga Arewacin Najeriya da ke kai wa kudancin Najeriya sun janye jigilar albasa zuwa yankin har sai abin da hali ya yi.

Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da ‘yan ƙungiyar IPOB suka tare wasu manyan motoci biyu na Albasa daga Arewa suka rabawa mutanen su.

Alhaji Halilu Muhammad Jaɓɓe, mai albasar da aka yi wa ɓarna a kudu maso gabashin Nijeriya ya bayyana wa BBC cewa a lokacin da aka kai wa motocin hari, jami’an tsaro sun kai musu dauki inda kuma su ka yi ta bata kashi tsakaninsu da mutanen da ake zargi da kai harin.

“Saboda haka mun janye kai Albasa a kudancin Najeriya har sai baba ta gani”. Inji shi.

Shin ya kuke kallon wannan mataki da suka dauka ne?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here