Sanannar Kungiyar Siyasa mai suna Baba Buhari For All, ta mika tallafin shinkafa buhu dubu goma ga Gwamnatin Jihar Katsina domin rarraba wa ga mabukata a wannan lokaci na watan Ramadan.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal ne ya karbi tallafin daga Shugaban Kungiyar na Jiha a madadin Gwamna Aminu Bello Masari.

Alhaji Muntari Lawal ya bayyana tallafin a matsayin wanda ya zo dai-dai da lokacinda make bukatar shi, lura da yanayin da al’umma suke ciki.

Shugaban Ma’aikatan ya ce za’a rarraba tallafin shinkafar ne ga masu gudun hijira a Kananan Hukukomin da matsalar tsaro ya shafa da sauran mabukata da marayu.

Daga nan sai ya bukaci wadanda za’a dora wa alhakin rarraba shinkafar akan su kasance masu gaskiya da adalci tare da sanya tsoron Allah a lokacin gudanar da aikin da aka Dora masu.

Tunda farko, Shugaban Kungiyar ta Baba Buhari For All na Jihar Katsina, Wanda Kuma shine Dan Majalissar Tarayya na Malumfashi da Kafur Alhaji Babangida Ibrahim Talau, ya ce tallafin na daya daga cikin ayyukan jin kan al’umma da Kungiyar ke gudnarwa a cikin watan Ramadan.

Alhaji Babangida Talau Wanda Shugaban Karamar Hukumar Malumfashi Maharazu Dayi ya wakilta ya ce, buhu 6000 ne aka kawo a cikin garin Katsina, a yayinda aka ajiye 4000 a Malumfashi domin rarrabawa ga Kananan Hukukomin da zasu amfana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here