Advert
Home Uncategorized Kungiyar Afenifere Da Jaridar Sahara Reporters Sun Yi Izgili Ga Musulunci

Kungiyar Afenifere Da Jaridar Sahara Reporters Sun Yi Izgili Ga Musulunci

A kokarin bai wa dan tawayen nan da ke kokarin kafa kasar Yarabawa zalla ta hanyar tashe-tashen hankula da jagorantar kashe mutanen da ba su ji ba ba su kuma gani ba kan shari’ar da ake yi masa a kasar Cotonou, wato Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, kungiyar kare kabilar Yarabawa ta Afenifere, ta yi izgili ga Musulunci kuma jaridar Sahara Reporters ta labarto.

Jaridar ta labarto cewa; Jare Ajayi, Sakataren yada labarai na kungiyar Yarabawa ya kwatanta gudun tsoron da Sunday Igboho ya yi yunkurin yi zuwa kasar Jamus ta jirgin sama ta hanyar amfani da fasfon karya ta kasar Cotonou da hijirar da fiyayyen Halitta Manzon Allah (SAWWA) ya yi daga Makkah zuwa Madina a lokacin da tsanani ya yi yawa.

Irin wannan misali da kwatance da kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta yi da wannan shakiyyin mutum kuma matsoracin gaske wato Sunday Igboho da kuma Salihin Bawa, Manzonmu kuma fiyayyen halitta, farin Jakada (SAWW), tabbas cin fuska ne ga Musulman duniya ku san Biliyan uku baki daya ba wai kawai ga Musulman Nijeriya ba. Kuma cin zarafi ne ga fiyayyen Halitta (SAWW).

Kuma sam bai kamata Jaridar Sahara Reporters da ake kyautatawa zaton sun karanci aikin Jarida a ilmance su nakalto labarin da aka iya hargitsa duniya ba.

A matsayinmu na Musulmai zamu dauki wannan rahoto a matsayin cin mutunci da 6atanci ga Musulunci domin yin hakan ta6a halittar da ta fi kowacce halitta daraja ce a duniya da lahira.

ME YA KAMATA MU YI?

1. A matsayinmu na wayyayun mutane, wanda addinin mu ya koyar damu natsuwa da kuma aikata kyakkyawan aiki, sannan ga shi Jaridar nan a shafin sada zumunta na Facebook, Intagram da Twitter take, kuma a nan suka nakalto labarin nan, sannan mu ma gamu nan miliyoyi a shafin, akwai bukatar mu yi tururuwa wajen kai karar su ga hukumar Facebook, Twitter da kuma Instagram, domin ganin sun goge shafin na su, ko kuma su goge wannan rahoton.

2. Akwai bukatar mu sanyawa kawukanmu daina bibiyar shafin ta hanyar ‘unfollowing’ dinsu wanda hakan zai sanya su rasa adadin mabiya masu yawan gaske.

3. Bari na ba ku misali; a watannin da suka gabata, akwai wani shafi a Facebook ana ce masa NAS ACADEMY, shafin na labarto labarai ne cikin bidiyo na abubuwan da ba a saba gani ba, da na ban al’ajabi tare da horas da mutane akan abin da ya shafi yadda ake hada bidiyo da sauran su, wanda hakan ya bai wa shafin damar samun miliyoyin mabiya. Sai dai kwatsam a yayin ta’addancin Haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ga raunanan Falasdinawa a watanin baya, sai mai shafin ya bayyana ta’addancin na HKI a matsayin wai ‘rikici ne tsakanin Isra’ila da Falasdinawa’, hakan ya sanya cikin Awa 24, mabiyansa suka koma mutum miliyan 20 daga mutum miliyan 38. Wannan kishi ne ga al’ummar Falasdin da al’umma masu Dattako suka nuna. Akwai bukatar mu ma mu dauki irin wannan matakin na yin ‘Unfollowing’ shafin Jaridar SAHARA REPORTERS bisa nakalto labarin nan na cin zarafi.

4. Akwai bukatar a samu mutane masu kishin addinin nan su ba shi kariya ta hanyar maka kungiyar Afenifere a kotu da ta kwatanta gudun tsoron matsoracin nan wato Sunday Igboho da Hijirar Manzonmu (SAWW). Haka zalika da maka Sahara Reporters a kotu da ta nakalto labarin nan, a nemi su bai wa duniyar Musulmi hakuri tare da goge labarin, su kuma Afenifere su janye kalaman na su, tare da bada hakuri da kuma alkawarin ba za su sake wannan gangancin ba a nan gaba, domin Musulmi ba za su lamunci hakan ba.

5. Akwai bukatar mutane su yi aikin wayar da kan Musulmi da masu kishin ‘yan Adamtaka da suke amfani da shafukan sada zumunta din nan da na ambata wajen a yi ta kai karar Sahara Reporters har sai an dau mataki akan su. Ka da abin ya yi ‘trending’ na wani lokaci a kuma manta da shi kwata-kwata ba tare da an gigita su ba.

6. Mutane a daidaikunsu da kuma kungiyoyinsu su yi ta rubutun Allah-wadai da kungiyar Afenifere bisa wadannan kalamai tare da kiran Jaridar Sahara Reporters su goge labarin. A kikkira tarukan manema labarai, a yi magana ta hankali, maganar ta gamayye ko’ina dangane da wannan batun a cikin gari da kafafen watsa labarai, har sai kowa ya fahimci lamarin nan da hatsari da kuma muhimmancin dake cikinsa.

-Ammar M. Rajab
27072021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: