Kungiyar AC Milan ta dauki dan kwallon Croatia, Mario Mandzukic zuwa karshen kakar tamaula ta bana. Bbc
Dan wasan ya koma Milan a matakin wanda bai da yarjejeniya da wata kungiyar, ya kuma sa hannu da za a iya tsawaita zamansa idan ya taka rawar gani.
Tsohon dan kwallon Juventus, mai shekara 34 bai da wata kungiya tun bayan da ya bar Al Duhail ta Qatar a karshen kakar da ta wuce.
Dan wasan ya lashe Champions League a Bayern Munich a 2013 da kofin Serie A hudu a Juventus ya kuma buga tamaula a Atletico Madrid.
Mandzukic ya ci wa Croatia kwallo a gasar kofin duniya a wasan da Faransa ta yi nasara da ci 4-2 ta zama zakara a 2018 a Rasha.
AC milan ce ta daya a kan teburin Serie A na bana da tazarar maki uku tsakaninta da Inter Milan ta biyu.