Advert
Home Sashen Hausa Kungiya Mai Fafutukar Ganin An Samu Sabuwar Jahar Katsina Mai Suna Project...

Kungiya Mai Fafutukar Ganin An Samu Sabuwar Jahar Katsina Mai Suna Project New Katsina Sun Ziyararci Radio Najeriya Companion FM reshen Jahar Katsina

*Kungiya Mai Fafutukar Ganin An Samu Sabuwar Jahar Katsina Mai Suna Project New Katsina Sun Ziyararci Radio Najeriya Companion FM reshen Jahar Katsina*

Daga Zahraddeen Sirajo Abbas

@Katsina City News

Kungiyar *Katsina New Project* ta kai ziyara a Gidan Radio Najeriya reshen Katsina, a wannan Rana ta Talata 21 September 2021, da misalin 11:30 na safe, bayan addu’ah kowa ya gabatar da kanshi in da daga bisani jagoran wannan kungiya Comrade Umar Sabiu Sukuntuni ya fadi makasudin zuwan “mun zo domin kawo ziyara, tare da fahimtar juna, da neman shawara.

Ya kara da cewa mun kafa wannan kungiya ne domin kiran matasa akan abunda ya shafi inganta rayuwa fara daga ilimi, tunani, tare da yunkurin kawo gyara akan lamuran da suka shafi siyasa, tare da yin tunani da amfani da ilimi wajen zaben shuwagabanni nagari.

A cikin wannan tafiyar tamu, tafiya ce ta masu ilimi, mafi yawan mutane wannan kungiya Malamai ne na Jam’iah wadanda mafi yawansu suna da matakin (Degree) na ukku, akwai ‘yan Jarida, yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati da kuma shuwagabanni kungiyoyi.

Mun zo domin tattaunawa tare da kara ma juna ilimi akan halin yau da kullum tare da tunanin hanyar da zamu bi wajen inganta rayuwa, fara daga barin munanan dabiu, shaye shaye, siyasa da harkokin yau da kullum.

Daga cikin waɗanda suka tabi masu ziyarar, sun hada da Shugaban gidan Radio na Jahar Katsina Alh Mutktar Abubakar Dutsinma, Mujjitfha Tanimu, Musa Adamu, Secretary, cashier, da kuma Admin Secretary.

A cikin jawabin nasa Alh Mutkhtar Abubakar Dutsanma ya fara da cewa “Alhamdulillahi, bayan yabo da godia ga Allah, mun ji dadi ganin yadda wannan kungiya ta kalli cewa zamu bada gudunmuwa har kuka yi tunanin cewa bari ku kawo mana ziyara.

Yana da kyau ga Matashi yasan halin da abubuwa suka kasance a jiya da yau da kuma tunanin Gobe, misali idan muka kalli Arewa zamu iya cewa mun zama (Saniyar Ware) abun mamaki har yanzu tunaninmu ya kasa wuce Abinci, ina ake sayar da Alkubus, Dan Wanke, ko ina wane ke aiki ko mace ta yi wa Mijinta ko kishiyarta Asiri.

Kowa yasan cewa Katsina gari ne da ya shan banban da sauran garuruwa, to yakamata ace mun fito da wani tunanin wajen kiran Matasa da tunanin mafita akan harkar shaye shaye da ta addabi matasa wadda kuma ita ce musabbabin wa’inan matsalolin da muke ciki a yau.

Sanin kowa ne cewa akwai (Bata garin yan siyasa wadanda kullum tunanin su bata matasa), wannan aikin da kuka dakko lallai babban aiki ne da yake bukatar jajircewa musamman akan kokarin kawar ma al’umma wani abu da suka saba da shi.

Zan baku shawara akan kuyi hakuri ku jajirce, kuma ku sani zaku samu kalu bale har wajen yan siyasa saboda aikinku zai zama kamar suna aiki kuna warewarewa ne, aiki ne na gyaran akida, tunani, da kuma hali.

Ya kamata wannan aikin naku ya fara tun daga makarantar Firamari, ya zama na cewa ko yaro ya taso da tunanin kishi da kuma son gina jaharsa da al’mmarsa.

Shirye muke mu baku gudunmuwa wajen yada shirinku da aikinku, muna tabbatar maku mun shirya Dari Bisa Dari, abun ya shafi taro ne ziyara ce ko wani gangani ne inshallah zamu bada gudunmuwa.

Daga karshe ina baku shawara ku yi taka tsantsan wajen abubuwan ku duk da cewa dole sai an rabi Gwamnati da Yan Siyasa, muna addu’ah Allah Ya sanya wannan aikin naku ya kawo karshen wannan matsalolin da suke adabar Gwamnati da Al’mma.

Daga karshe Dan Jarida Abubakar Yunusa Dutsinma ya neman ma kungiyar damar shigowa da wasu daga cikin ma’aikatan wannan gida cikin wanan kungiya domin yin aiki kafada da kafada, wannan aikin namu yana bukatar yan Jarida a kowane janibi, daga karshe Shugaban ya aminci da wannan bukata kamar yadda aka nema*.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: