KUNA BIN MU BASHIN GODIYA, ƘOFAR NUMFASAWA GA ƳAN TA’ADDA DA MIYAGU, SHUGABA BUHARI YA FADI WA SOJOJI DA SAURAN HUKUMOMIN TSARO.

KUNA BIN MU BASHIN GODIYA, ƘOFAR NUMFASAWA GA ƳAN TA’ADDA DA MIYAGU, SHUGABA BUHARI YA FADI WA SOJOJI DA SAURAN HUKUMOMIN TSARO.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Alhamis a Maiduguri, jihar Borno, yace Jami’an Soji maza da mata da Sauran Hukumomin tsaro da a halin yanzu ke kokarin Kawo karshen kalubalen tsaro a Ƙasar, na bin Najeriya bashin Godiya, Musamman wadan da suka rasa rayuwar su, Shugaban yabada tabbaci ga Iyalan su cewa Gwamnati zata cigaba da Tallafa wa dukkanin Iyalan su.

Shugaban kasar, a Ziyarar aikin daya kai wa Sojoji da Sauran Hukumomin tsaro a Cibiyar Yakin HADIN KAI dake da matsuguni a Barikin Maimalari, ya hori Sojoji da Sauran Hukumomin Tsaro da kada su bar koda Gurin Numfasawa ga Ƴan ta’adda da Miyagu dake sassa daban daban a Fadin kasa, Shugaban yace dole ne sai an kammala yakin da aka fara da maido da zama lafiya da sake gina dukkan inda yakin ya shafa.

“Nayi farin cikin kasan cewa tare daku a wannan rana, domin yi muku jawabi kan wannan ziyara tawa ta musamman a Jihar Borno, Zan so nayi amfani da wannan dama domin sanya wannan cikin Tarihi cewa har abada Kasar mu tana muku Godiya, kan nuna kishin kasa da jajircewa Gurin bada kariya ga Ƙasar Mu daga Miyadu da Masu tada ƙayan baya da.

“A saboda haka ina yaba muku da tuna dukkan Jami’an da suka sa daukar da Rayuwar su don tabbatar da cewa Ƙasar Najeriya ta cigaba da wanzuwa cikin tsaro.

“Kamar yadda na mika sakon Alhini da Ta’aziyya ta ga Iyalan Gwarzayen mu da suka fadi ƙasa na kuma yi addu’a Allah yaji kan wadan da suka rigaye mu, Ina son Na tabbatar muku Cewar, Gwamnati na zatayi dukkan kokari da samar da abinda ya dace domin tabbatar da cewa ƴaƴa da Iyalin Gwarzayen mu da suka fadi kasa a yayin tsaron Kasar mu abin kauna, an basu dukkan kulawa data dace,” Cewar Shugaban.

Shugaban yace Gwarzayen mu da suka samu raunuka dasu samu kulawa ta musamman har sai sun warke sun samu cikkakken lafiya.

“Yayin dana yabi irin kokarin ku na baidaya Gurin take da rage karfin Ƴan ta’adda da sake tabbatar da bada kariya ga Mulkin Kasar mu, Ina kuma fatan ku kara fadada hakurin ku da kokari na rashin gajiyawa a lokacin fuskantar wahalhalu da kuke yi a yayin aiwatar da aikin ku.

“Kokarin ku na bai daya ya haifar da Ɗa mai Ido Gurin samun zaman lafiya da muke jin dadin sa a halin yanzu a wannan yanki. Akan Idona, Jami’an tabbatar da tsaron Najeriya an Samar musu da tsari mai ƙarfi da sanar da hanyar bullewa domin tsaron Mulki da Mutuntakar Kasar mu.

Shugaban ya kara da cewa “Kada mu bari ko banbanci ka Kofar Numfasawa ya zamo mana kalubale ko rushe bukatar Kasar mu da Dabi’un ta. Tsaro da Hukumomin Jami’an ta suji tabbaci a zukatan game da kokarin Gwamnatin Tarayya na ganin an samu nasara a yaki da ake da Ta’addanci da Miyagu,”

Shugaba Buhari ya yabi Sojoji da Hukumomin Tsaro kan aikin hadin Gwiwa wanda hakan ya haifar da Nasarori Gurin maido da zama lafiya da bin doka da oda.

“Ina farin ciki musamman kan yadda na lura cewa ana samu Karuwar fahimtar juna da hadin kai tsakanin Jami’an Soji, dama kuma Sauran Hukumomin hadin kai gurin yaki da Ƴan Ta’adda da Sauran Miyagun ƴaƴa a yankin Arewa maso Gabas.

“Nasarori da aka cimma ya zamo shaida Sakamakon wannan aikin hadin gwiwa wanda aka cimma a Yakin TURA TAKAIBANGO wanda kawo yanzu ya kawo koma baya sosai ga Ƴan tada kayan baya kan yanda suke aika aika a yankin Timbuktu da Dajin Sambisa dama yankin Tafkin Chadi.

A sakamakon haka ina farin cikin gane cewa Soji da Sauran Hukumomin Tsaro ciki harda na masu ruwa da tsaki a fararen hula kan yanda suke fahimtar gaskiyar salon yaki mai taken HADIN KAI wanda kamar yadda sunan ke nuni dashi “Hadinkai, hadin gwiwa da bada hadin kai.”

“Ha hanyar aiki gaba daya ta abinda kenan dama dama da muke dasu da hanyoyi daban daban na Hukumomin tabbatar da tsaro da Sauran Jami’an tsaro, Muna fatan Makiyan Kasar mu zasu ji a jikin su na nauyin irin makamai da muke dasu don warware Matsalar mu.” inji Shugaban kasa.

Kokarin Yin aiki kafada da kafada na Hukumomin da Sauran Jami’an tsaro, Shugaba Buhari ya bada tabbaci cewa Gwamnatin sa tana kokarin samar da wani tsaro na bayan-yaƙi da sake Maimaitawa dama gina zama lafiya.

“Ana kan Kokari na baidaya na sake Maimaita da fito da Shirye Shirye a gaggauce a garuruwa da yaki ya shafa a yankin Arewa maso gabas.

“Ina fata cewa wannan zaisa a maida Ƴan gudun Hijira guraren su cikin gaugawa, dama kuma sake maido da rayuwa ya daidaita don mutane su koma gidajen su a garuruwan su na asali.

“tare da Cigaban kasuwanci da sake gine gine, zamu ci gaba da bada dukkan abinda ya dace ga Jami’an tabbatar da tsaro ta hanyar da komi zai dai dai ta,” Inji Shugaban.

Shugaban kasa yace aiyuka da dama na Gwamnatin Tarayya yayi sanadin sayo da kawo manya manyan kayan yaki, ciki harda makamai da albasurai na yaki:

“Da yawa ciki an sanya su yaki da ake haka kuma nan gaba kadan saura kayakin aiki wanda basu jima da aka kawo su Kasar ba, za’a bada su ga Jami’an tsaro. Za’a kara sayo kayakin aiki bila adadin ga Jami’an tsaro domin kawo karshen makamai na kusa da masu Dogon zango.

“a dai de wannan gaba Zan so kuma na yabawa Shugabannin Tsaro kan yanda suke tsaro da hangen don tabbatar da cewa wasu cikin muhimman kayakin yakin mu an samu kera su a cikin Kasar mu.”

Shugaban kasa Buhari ya kuma lura cewa yanzu a gida Najeriya ake gyara da duba lafiyar wasu cikin Makaman yaki ta haka ana rage wa kasar dawainiyar kashe kudade dama kuma Samar da guraben aiyuka ga dubban Al’ummar kasa.

“Jami’an Sojin mu da Sauran Hukumomin tsaro, ya zamo dole ku fahimci cewa wadan nan kayakin aiki da aka sayo su zasu samu kulawa da aiki da su ta yadda ya dace akan Ƴan Ta’adda da Sauran Miyagu. Babu wani damar Jindadi da za’a basu, babu bukatar sai an fada muku kuzamo cikin shiri a koda yaushe.

“A matsayi na na Babban Askarawa naku, Ina son Na baku tabbaci cewa Gwamnati na zata ci gaba da aiki domin Samar da kudade akan lokaci daya kamata da sayo kayakin yaki ga Jami’an soji da Sauran Hukumomin tsaro. Wannan anyi ne da nufin kara habaka yaki da ake ciki yanzu don akawo karshen sa dama cewa bukatar mu na bai daya da zama lafiyar mu.

“Bugu da kari, jin dadin ku Shine abinda yafi komi anfani da nuna damuwa a kai ga wannan Gwamnati. Naji dadi cewa an fara sake fasalin aiki ga Sojoji da suke bakin daga, kamar yadda na bada Umarni. Ina da tabbaci cewa hakan zai kankantar dama kuma yiwuwar kawo karshen dabarun yaki, dama kuma kara karfafa Ƙwarin gwiwar Sojoji, inji Shugaban.

Shugaban kasa ya godewa wa Sojojin da Sauran Hukumomin tsaro kan rashin bada koma fa son biyayya da sonkai a yayin da ake aikin tsaron kasa, ya kara da cewa. “Ƙwarin Gwiwa da Damarku zai ci gaba da burge wasu, don su gaje ku anan gaba.”

“Yayin da na yaba kan Jajircewar ku, bari kuma na tunatar daku cewa har yanzu akwai jan aiki dake gaban ku, domin kammala maido da zama lafiya a yankin Arewa maso Gabas, da durkusar da aiyukan barayin daji a yankin Arewa maso Yamma, da Arewa ta Tsakiya, dama magance Sauran kalubalen tsaro dake a Fadin kasa.

“A saboda haka ya zamo dole ku tsaya da gaske don ganin wannan yaki yazo karshe. Yayin aiwatar da haka, dole ku bada karfi ga aikin hadin gwiwa, da karfafa aiki tare da Jami’an soji na Sauran kasashe Makwabta Jamhoriyar Kamaru, Chadi, Nijar Gurin yaki tare da mukeyi dasu kan Ƴan ta’adda, karkashin shirin Yakin hadin Gwiwa, Multinational Joint Task Force. Hakan zai taimaka wa kokarin ku da dai dai ta al’amura a yakin,” inji Shugaban.

Ya bukaci Soji da Sauran Hukumomin tsaro dasu sa muyi Alfahari da ƙasar mu Najeriya.

Shugaban kasa Buhari, ya kuma gana da wasu cikin Jami’an soji da suka samu raunuka ya basu tabbaci cewa Gwamnatin ta zaku taga sun samu sauki da jin dadi su.

Cikin jawabin sa, Babban kwamanda na Yaki mai taken HADIN KAI, Maj Gen. Felix Omoigui, ya bada tabbaci wa Jami’an soji kan tabbaci da yake dashi kan kokarin Shugaban kasa Gurin Jin dadin su, Musamman Gurin kawo karshen yaki da ake yi.

Kwamanda ya godewa Shugaban kasa kan wannan ziyara daya kawo wa Sojojin, wanda yace haka zai kara habaka Ƙwarin gwiwa ga wadan da ke yaki domin Samar da zama lafiya a Ƙasar.

Gwamnonin jihohin Borno da Yobe, Babagana Zulum da Mai Mala Buni, Babban Hafsan Tsaro na Ƙasa Gen. Leo Irabor da Babban Hafsan Sojin Kasa Maj. Gen Farouk Yahaya da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Rear Admiral Awwal Gambo da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Vice Marshal Isiaka Amao da Mai baiwa Shugaban kasa Shawari akan Harkan Tsaro, Maj Gen. Babagana Monguno mai ritaya sun kasan ce a Gurin Ziyarar.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
17 ga watan Juli, 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here