Advert
Home Sashen Hausa KU MURKUSHE YAN TA ADDA..inji masari

KU MURKUSHE YAN TA ADDA..inji masari

KU MURKUSHE YAN TA ADDA..inji masari

Daga abdulhadi bawa

Kakkabe ta’addanci ta hanyar murkushe ‘yan ta’adda da samar da dawwamammen zaman lafiya ga al’umma shi ne babban kalubalen da ta tasa a gaba kuma take fatar samun nasara, hadin guiwa da jami’an tsaro.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana haka yau, a Abuja, yayin da ya kai ziyarar aiki Hedikwatar rundunar Sojojin sama ta Najeriya. Gwamnan, wanda babban hafsan mayakan Saman Air Marshal isiaka Oladayo Amao ya tarba, ya kara da cewa wannan ziyara ba ita ce ta farko ko ta biyu ba a jerin ziyarorin da ya kawo ma wannan runduna ba, duk domin samar da tsaro ta hanyar dakatar da ayyukan ta’addanci.

Alhaji Aminu Masari ya bayyana wa Air Marshall cewa, wannan matsala ta faro ne da satar shanu da kuma kisan al’umma nan da can, amma a lokacin da Gwamnati ta dauki matakan dakile satar shanu da kuma yin sulhu da wasu daga cikin barayin shanun, sai abin ya canza salo.

Garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa da sauran munanan ayyukan dake keta haddi da mutuncin mutane sukayi kamari. Wannan ya sanya Gwamnatin Jiha ta yanke shawarar ba za ta kara zama da wadannan ‘yan ta’adda ba, idan har suna da bukatar a tattauna dasu, to su nemi jami’an tsaro sannan kuma su nemi aminci da sulhu da mutanen da suke cuta mawa ba dare ba rana.

Ya kara da cewa gudummawa ta sauran tallafi da Gwamnatin Jiha take ba jami’an ba za ta daina, za ma ta iya karawa idan har bukatar hakan ta taso, ma damar al’umma za ta zauna lafiya cikin aminci da kwanciyar hankali.

A nashi bangaren, babban hafsan mayakan saman Air Marshall ya yaba wa Gwamnan a kan irin kai kawon da yake domin samar ma al’umma zaman lafiya. Ya kara da cewa suna sane da irin muhimman matakan da Gwamna Masari ya dauka yake kuma kan dauka, musamman yanda ya gitta rayuwar shi, ya cikin dazuzzukan da ‘yan ta’addan suke zaune domin yin sulhu tsakanin su da mutanen karkara, duk kuwa da cewa ‘yan ta’addan sun ci amanar wannan sulhu, ga kuma dauki kala kala da Gwamnatin Jihar take kai ma jami’ an tsaro akai akai.

Air Marshal Amao ya bayyana cewa aikin da rundunar ta fara a garin Katsina na kafa mazauni na dindindin wanda ya hada da gina filin safka da tashin jiragen sama yana ci gaba da tafiya, haka kuma aikin karamar tashar jiragen sama da ake yi a garin Funtua shi ma yana tafiya yadda ya kamata kuma a shirye suke domin tabbatar da an kammala su cikin lokaci domin samun damar kai dauki cikin hanzari.

Ya kuma tabbatar ma Gwamna Masari cewa in sha Allah, nan ba da jimawa ba za su dakile wannan matsala da taki ci taki cinyewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

COURT IN KATSINA CONVICTED INTERNET FRAUDSTERS.

@ katsina city news The Kano Zonal Command of the Economic and Financial Crimes Commission today August 5th, 2021 secured the conviction of eight internet...

Rashin tarbiya; Dalibi ya daba wa malaminsa wuka har lahira, saboda kawai malamin ya yi masa bulala

A makarantar sakandaren koyar da fasaha dake Bukuru ‘Government Technical College Bukuru (BUTECHS)’ dake jihar Filato ne wani dalibi ya kashe malaminsa saboda malamin...

Ƴan Bindiga Sun Sace Mahaifan Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim,Gusau "Yan bindigar sun mamaye garin Magarya garin kakakin majalisar jihar Zamfara Nasiru Mu'azu Magarya da yammacin ranar Laraba inda suka yi awon...

Kowa Na Da Rawar Da Zai Taka Wajen Samun Dawammamen Zaman Lafiya A Najeriya, Gwamna Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa ba jami'an tsaro ba ne kadai ke da hakkin samar da tsaro a kasar...
%d bloggers like this: