Ku Guji Yin Tazarce – Buhari Ya Ja Kunnen Shugabannin Kasashe

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya shawarci shuwagabannin ƙasashen duniya da kada su yi riƙo da madafun iko bayan wa’adin mulkin su na tsarin mulki.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake jawabi sama da shugabannin duniya 80 a wurin babban taro na 76 na Majalisar Ɗinkin Duniya a New York.

Buhari ya yi kalaman ne ƙasa da shekaru biyu ga zaɓen 2023 inda ake sa ran zai miƙa mulki ga Shugaban Nijeriya na gaba bayan shekaru takwas a Aso Rock.

Buhari, wanda kuma ya kasance tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja tsakanin 1983 zuwa 1985, ya kasance zaɓaɓɓen shugaban Nijeriya na dimokuraɗiyyar tun daga 2015.

Amma, ya sake nanata cewa, Nijeriya tana goyon bayan ƙoƙarin da nahiyoyi da na yankuna ciki har da Ƙungiyar Tarayyar Afirka da Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka suka yi don magance matsalar.

Da yake jawabi ga shugabannin duniya ciki har da sabon Shugaban UNGA, Abdulla Shahid na Maldives, Buhari ya ce, “A Yammacin Afirka musamman, nasarorin dimokraɗiyyar da muka samu cikin shekarun da suka gabata a yanzu ana lalata su.

Al’amarin da ya faru na karɓe ikon da bai dace da kundin tsarin mulki ba, wani lokacin don mayar da martani ga sauye-sauyen tsarin mulki na wasu shugabanni, bai kamata ƙasashen duniya su amince da su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here