*Ya Bada Lambar Yabo Ga Ressa Hudu Na Hukumar da Jami’ai 25 Saboda Koƙarinsu

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya ya buƙaci jami’an hukumar da su ƙara matsa lamba musamman ga dillalan miyagun ƙwayoyi, masu safarar su da kuma kungiyoyin su a shekarar gobe, 2022.

Marwa ya bada wannan umurni ne a yau talata, 21 ga watan Disamba, 2021, a wani zama na musamman da yayi da daraktoci, kwamandojin shiyoyi jihohi, da yankuna na musamman inda aka bada lambar yabo ga jihohi guda hudu tare da bada lambar yabo da kyautar kudi ga jami’ai 25 musamman saboda hazaka da kokari da suka nuna a fagen yaki da miyagun kwayoyi a bangarorin bukatuwar miyagun kwayoyi (Drug Demand Reduction) da safarar miyagun kwayoyi (Drug Supply Reduction), tare da ingantaccen kalubalantar masu laifi a gaban kotu a karshen shekarar 2021. Marwa yayi amfani da wannan dama wajen yabawa shugaban Muhammadu Buhari saboda goyon baya na din-din-din da yake baiwa hukumar ta NDLEA.

A cewar sa, alkaluman bayanai na ayyukan hukumar na dakile safarar miyagun kwayoyi (Drug Supply Reduction), yayi tashin gwauron zabi zuwa káme 11,340 tare da nasara a kotu na kyas 1,111 a cikin watanni 11. Kazalika a fannin rage bukatuwar miyagun kwayoyi, an samu nasarar tsugunarwa tare da bada shawara ga mutane 7,066 a cikin watanni 11. Haka kuma an yi nasarar kwato miyagun kwayoyi wanda yawan sa ya kai Kilograms miliyan uku da digo uku daga kan titi a cikin kasar nan, wannan na nufin raguwa matuka a fannin kwayoyi da ‘yan ta’adda suke amfani da su da ma mutanen gari.

“Wannan lambar yabo da kuma takaddun jinjina alama ne na cewa shugabancin hukumar NDLEA ta tabbatar da nata bangaren ta hanyan bada kwarin guiwa da zaburarwa ga jami’ai , a kokarin ta na tsamo hukumar daga kangin da ta samu kanta a baya. Wannan yasa muka kirkiro da shirin bada lambar yabo na wata-wata ga rehen da ta nuna hazaka, wanda daga baya muka mayar da shi wata uku-uku. Wannan kuwa mun yi shi ne don sakawa kokarin jami’ai da kuma reshen da suke.

“Ba zai yuwu ace wannan kokari namu na bada lambar yabo bai haifar da ɗa mai ido ba, musamman idan akayi la’akari da cewa wannan kokari ya zaburar da hukumar inda yanzu tasirin aikin ta ya ƙara fitowa fili, wanda a koda yaushe yake janyo mana yabo daga ciki da wajen Nijeriya. Ko a mako uku da suka gabata, a taron ICPC na uku wanda ya gudana a ranar 30/11/2021, jami’in mu ya zama daya daga cikin mutane uku da shugaban kasa da kan sa ya baiwa lambar shaida na nagarta a aiki na shekarar 2021. Wannan kadai yana bayyana sabuwar tsarin aiki na hukumar na ɗabbaƙa nagarta. Saboda wannan kokari nasa, ya cancanci mu yaba masa bisa nasarar samun shaida a matakin ƙasa.

“Shugabancin NDLEA a yanzu yayi nasarar kau da zaman dirshan na mukamai kusan gabadayan ta. Mun gyara tsarin muƙaman mu tare da ƙarin girma ga jami’ai 3,506. Mun daukaka jin dadin ma’aikatan my, sannan mun samar musu da tsarin inshora. Mun biya iyalan wadanda suka rasa ran su, mun ninka karfin ma’aikatan mu a wannan shekara. Zamu samar da bariki a shekarar da zamu shiga, wanda dole mu godewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari akai. Akwai sauye-sauye da dama da suke gudana yanzu. Hukumar na ƙoƙarin dawo da martabar ta da ƙimar ta kamar sauran hukumomin gwamnati.

Muna iya ƙokarin mu na ganin cewa mun samu nasara a yaƙi da miyagun ƙwayoyi da safarar su. Mun ƙaddamar da manyan tsari biyu: NDCMP da kuma shirin yaƙi da miyagun ƙwayoyi (WADA) a jihohi 36 na Nijeriya. Saboda haka yanzu ya rage gare mu, mu tabbatar da cewa waɗannan nasarori sun cigaba ba wai su tsaya ba. Zan iya tabbatar mana da cewa zamu iya hasashen cigaba ba tare da fargaba ba. Muna da yaƙinin cewa abubuwa zasu ƙara kyau. Saboda haka, dole mu cigaba da tunatar da kanmu cewa ayyukan mu su ne zasu kyautata wanann tafiya ta kawo karshen miyagun ƙwayoyi a Nijeriya.

Mahmud Isa Yola
Hedikwatar NDLEA, Abuja
Talata, 21 Disamba, 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here