Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa ba jami’an tsaro ba ne kadai ke da hakkin samar da tsaro a kasar nan, kowa na da rawar da zai taka wajen ganin an dawamammen zaman lafiya.

Masari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban rundunar sojan kasar Najeriya, Mejo Janar Yahaya Faruq a gidan gwamnatin jihar Katsina a yau Alhamis.

Gwamna Masari ya ci gaba da cewa duk da wasu kananan hukumomi goma ana kai masu hare-haren kusan kullum, amma a halin yanzu ana samun sauki.

Masari ya kara da cewa ya kamata sojoji su kara bunkasa bangaren kimiyya da fasahar Zamani, domin zai kawo karshen wadannan yan bindiga da masu satar mutane domin ganin an kawo karshen duk wani bata gari a kasar nan. Yan Najeriya suna son ganin sojoji sun koma barikokinsu, domin a bar yansanda ga al’umma.

Da yake jawabi, Shugaban Rundunar Sojan Kasa, Mejo Janar Yahaya Faruq, ya yaba wa gwamnan Jihar Katsina, na irin kokarin da ya ke yi wa sojojin domin ganin sun gudanar da aikin su a jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here