Kungiyar Izala reshen jihar Katsina ta nuna damuwarta kan yadda ta ce shuwagabannin al’umma da suka zaba sun gaza sauke nauyin alkawuran da suka daukar wa al’umma.

Shugaban kungiyar na jihar Katsina Shaikh Yakubu Musa Katsina shi ne ya karanta jawabin a lokacin gudanar da sallar Idi a masallacin GRA dake cikin birnin Katsina.

“Wani abu da yakamata yan siyasa su sani shi ne, lokacin zabe na ta ci gaba da matsowa, sannan abin da sheda ta tabbatar ta kafafen yada labarai da masallatai da wuraren jawabai shi ne, wadanda muka zaba ba su tsare abin da muka zabe su ba, ba su tabbatar da wakilcin da yakamata ba, saboda haka su shirya za su dawo wurin jama’a don haka abin da muke so a fada wa jama’a minene ka yi wa kai mawa, kuma yaya ka yi, don mi za a sake zabar ka.

Shaikh Yakubu Musa ya ce a wannan karon fa babu maganar jam’iyya, za a duba sahihancin mutum ne a kowace jam’iyya kuwa ya fito

Kamar yadda DW Hausa ta wallafa faifan muryar Shehin Malamin da Katsina Daily Post News ta ji, Shaikh Yakubu Musa ya jaddada cewa, babu jam’iyyar da za su bi, Allah sahihin mutum ko a wace jam’iyya yake, nagarta da cancanta ce za a duba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here