Kotun Koli ta jaddada hukuncin soke jam’iyya 74 a Najeriya

Kotun Ƙoli a Najeriya ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara da ya soke jam’iyyun siyasa kimanin 74 daga cikin 92 da ake da su a kasar.

A shekarar da ta gabata ne hukumar zabe INEC ta soke jam’iyyun saboda rashin tabukawa a babban zaben kasar na 2019 .

Mai shari’a China Nweze da ya yanke hukuncin ya ce soke jam’iyyar NUP – daya daga cikin jam’iyyu 74 wadda kuma ta shigar da karar – an yi ne bisa tsarin doka da kuma tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa da dokar zaben kasar.

A yanzu dai wannan hukuncin ya tabbatar da makomar jam’iyyun da aka soke rajistarsu.

A ranar 29 ga watan Yulin 2020 ne kotun daukaka kara da ke Abuja, babban birnin kasar ta jaddada ikon da INEC ke da shi na soke rajistar jam’iyyun.

Mai shari’a Mohammed Idris a hukuncin da ya yanke, ya ce INEC ba ta yi kuskure ba wajen daukar matakin soke jam’iyyar NUP.

Kotun ta tabbatar da hukuncin mai shari’a Taiwo Taiwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wadda a cikin watan Mayu ta soke rajistar jam’iyyar NUP da wasu jam’iyyu 73 saboda saba sashe na 225(a) na kundin tsarin mulkin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here