Kotun Daukaka Kara ta rushe daukar yan sanda 10,000 da aka dauka bara

Kotun Daukaka Kara ta rushe daukar yan sanda 10,000 da aka dauka bara

Kotun Daukaka Kara ta rushe daukar yan sanda 10,000 da aka dauka bara

Kotun daukaka kara ta rushe gyaran dokar daukar yan sanda da aka gyara a wannan shekarar ta 2020 domin rage karfin hukumar ma’aikatan yan sanda ta kasa (PSC)

Kotun ta ce sabuwar dokar ta sabawa dokar yan sanda dake cikin sakin layi na 30 sashi na daya tsari na uku dake cikin daftarin dokokin kasa da aka yi wa gyara a 1999.

Haka kuma kotun daukaka karar ta kuma rushe daukar yan sanda dubu goma 10,000 da aka dauka a shekarar da ta gabata.

Hukuncin kotun na zuwa ne bayan da babbban Sufeton yan sandan Muhammad Adamu ya daukaka karar, sakamakon rushe batun daukar yan sandan da babbar kotun tarayya ta yi tun da farko

Kakakin hukumar Yan sandan ta kasa Ikechukwu Ani , ya ce sun sami kofin hukuncin Shari’ar a ranar Talata

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here