KOTUN DAUKAKA KARA
TA JIHAR KATSINA TA YI WATSI DA WANI ROKO DA MAHADI SHEHU YA GABATAR A GABANTA
-‐——————————————

Babbar Kotun sauraren daukaka kararraki ta jihar Katsina ta yi watsi da wani roko da Mahadi Shehu ya gabatar na neman ta soke dukkan aikin da Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta biyu dake nan Katsina ta yi, wanda ya hada da umurni ga jami’an yansanda cewa su kamoshi domin ya fuskanci tuhumar da ake yi masa a gabanta.

Maishari’a Abbas Bawale ne ya sanar da hakan a yayin da yake karanta bahasin Kotun a madadin Shugaban zaman sauraren daukaka kararraki na Dutsinma, Maishari’a Musa Danladi da kuma dayan wakilin Kotun, Maishari’a Ashiru Sani.

Maishari’a Bawale ya ce ba zai yiwu Kotun ta saurari irin wannan bukata a wannan mataki ba, tun da yake tana a cikin gundarin bayaninsa na daukaka karar da ya yi.

Sai dai kuma Kotun ta dakatar da Kotun Shari’ar Musuluncin daga cigaba da sauraren karar wadda Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina ya kai Mahadi Shehu akan zargin cin mutunci da bata masa suna, har sai an kammala sauraren daukaka karar da Mahadin ya yi.

Daga nan Maishari’a Bawale ya ce Alkalan sun tsaida ranar Litinin, 5 ga watan Yulin da mu ke ciki don soma sauraren gundarin daukaka karar, a Dutsinma.

Idan za a iya tunawa, Mahadi Shehu ya ruga Babbar Kotun ne bayan da ita Kotun Musulunci ta bada umurnin a kamo shi don ya kare kansa game da karar da Mustapha Inuwa ya kai shi.

Yayin da shi kuma Mahadin ya daga kara bisa koken cewa; Kotun Musuluncin ba ta bi ka’ida ba wajen sada shi da sammancin, wanda a cewar sa Masinjan Kotun ya kai masa a yayin da yake tsare a Hedikwatar Yansanda dake Abuja a madadin a iske shi a gidansa.

Sai dai kuma ita Kotun ta ce ta dauki matakin ne saboda sun neme shi a duk gidaje da wuraren sana’arsa ba a same shi ba. Kuma ta bi ka’idojin da koda a Inugu aka gan shi za a iya sada shi da sammacin.

Yanzu dai sai ranar Litinin din nan, 5 ga wata ake sa ran soma sauraren daukaka karar a zauren Babbar Kotun dake Dutsinma.

Abdullahi Yar’adua.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here