Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda

Maryam Sanda

Kotun Ɗaukaka Ƙara a babban birnin Najeriya ta kori ƙarar da Maryam Sanda ta shigar inda take so a hana aiwatar da hukuncin kisan da wata Babbar Kotu ta yanke mata.

Kotun ta jaddada hukuncin da Babbar Kotun ta Abuja ta yanke mata ta hanyar rataya sakamakon kama ta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

Yayin da yake yanke tabbatar da hukuncin ranar Juma’a, Mai Shari’a Steven Adah, wanda ya jagoranci alƙalai uku, ya ce kotun na da alhakin yin adalci kamar yadda doka ta tanada ba son zuciyarta ba.

A ranar 27 ga watan Janairun 2020 ne Mai Shari’a Yusuf Halilu ya yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa, wanda ya ce “ta hanyar rataya har sai ta mutu”.

An yanke mata hukuncin ne bisa caka wa Bilyaminu wuƙa, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Haliru Bello.

A shekarar 2017 ne aka fara gurfanar da ita a gaban kotu bayan mutuwar mijin nata a lokacin wata hatsaniya da aka samu tsakanin ma’auratan.

Ita dai Maryam ta musanta hannu a kisan mijin nata wanda ta ce ya zame ne ya faɗi a kan kuttun shisha inda tsagin kuttun ya cake shi a kirji har ya mutu.

Waiwaye

An soma zargin ta ne tun a Nuwamban 2017 da laifuka biyu da suka haɗar da kashe mijin nata Bilyaminu Bello.

A watan Disamban 2017 ne aka gurfanar da Maryam Sanda bisa zargin kisan mijin nata.

A lokacin da yake yanke hukuncin, alƙalin ya ce an samu dukkanin wasu shaidu da suka tabbatar da cewa Maryam ce ta aikata wannan laifi.

Ya kuma yi watsi da iƙirarinta na cewa mijin nata ya faɗi ne kan fasasshiyar tukunyar Shisha, abin da ya janyo mutuwar tasa.

Ya kuma bayyana cewa hujjojin da aka gabatar sun gamsar da kotu cewa ta caka wa mijin nata wuƙa ne yayin da faɗa ya kaure a tsakaninsu

A lokacin da alƙali ya zartar da hukuncin wadda ake tuhuma ta yi ƙoƙarin rugawa domin guduwa daga zauren kotun sai dai jami’an tsaro sun riƙe ta.

Bayanan bidiyo,Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here