Advert
Home Sashen Hausa Kotu ta yankewa Abdulrashid Maina Hukuncin Ɗaurin Shekaru Takwas a Gidan gyaran...

Kotu ta yankewa Abdulrashid Maina Hukuncin Ɗaurin Shekaru Takwas a Gidan gyaran Tarbiyya..

Zargin Almundahanar kuɗaden Pansho da suka kai N2.1Bn kotu ta yankewa Abdulrashid Maina Hukuncin Ɗaurin Shekaru Takwas a Gidan Maza.

Mai Shari’a Justice Okon Abang na Kotun Gwamnatin Tarayya dake Abuja ne a yau, November 8, 2021 ya yanke hukunci ga tsohon Chairman na wani Kwamitin gyaran yadda ake biyan kuɗin pansho wato Pension Reform Task Team (PRTT) a turance Abdulrasheed Maina akan ƙarar da take da nasaba da Almundahanar kuɗade Wanda Hukumar dake kula da yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gabatar a gaban kotun.

Alƙalin ya yanke hukunci ne bayan da Ɓangaren masu ƙara ya gabatar da hujjoji ƙarfafa da suka tabbas da laifin wanda ake zargin an kuma yanke mashi hukuncin ne akan ƙararraki 2, 3, 6, 7, 9 da 10 da aka gabatar ma Kotun.

Hukuncin zai fara Aiki ne tun daga Ashirin da Biyar ga watan Oktoba na Shekarar Dubu Biyu da Goma Sha Tara October 25, 2019.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Yansanda A Katsina Sun Chika Hannu Da Yan Kungiyar Asiri Biyu

Rundunar Yan Sanda Ta Jihar Katsina ta kame wasu matasa biyu da make zargin yan Kungiyar Asiri ne. Kamar yadda Jami'in Hulda da Jama'a na...

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...