Kotu ta yanke wa mai gabatar da shirin addini hukuncin daurin shekaru dubu

Kotu a Santanbul babban birnin kasar Turkiya ta yanke hukuncin daurin akalla shekaru dubu kan wani mashiryin shirin addini na gidan talabijin bayan samun sa da laifin aikata badala.

Tun a shekarar 2018 aka kame Adnan Oktar bayan gabatar da wani shiri mai cike da batanci da ya sabawa tanadin addinin Musulunci.

Baya ga lalata da manya da kananan yara, karin laifukan da kotu ta samu Oktar mai shekaru 64 da aikatawa sun hada da, damfara da kuma yunkurin satar bayanan sirri na rundunar sojin Turkiya da kuma ‘yan siyasa, abin da ya sanya kotun yanke masa hukuncin daurin shekaru dubu 1 da 75.

Yayin wani zama a watan Disambar 2020, Oktar ya shaida wa Alkali cewa yawan ‘yan matansa ya kusa dubu 1.

Tun shekarun 1990 Adnan Oktar ya soma jan hankalin jama’a, bayan samun kungiyar addinin da yake jagoranta dumu-dumu da laifukan da suka shafi lalata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here