Kotu Ta Wanke Tsohon Shugaban NNPC Andrew Yakubu Kan Badakalar Dala Miliyan 9.8.

Idan dai ba a manta ba, a shekarar 2017 ne hukumar dake bankado masu yi ma tattalin arzukin kasa zagon kasa ta EFCC ta kai samame gidan Mr. Andrew Yakubu da ke unguwar Sabon Tasha a jihar Kaduna, inda ta gano dala 9,772, 800 da fam 74,000 a wani ma’aji.

To saidai a yau Alhamis ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta wanke tare da sallamar Andrew Yakubu tsohon shugaban NNPC daga laifin almundahanar kudaden dala miliyan 9.8 da aka kama a gidansa a shekarar 2017.

Jaridar PremiumTimes ta ce, Hukumar ta gurfanar da shi a gaban mai shara’a Ahmed Mohammed na babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar 16 ga watan Maris na 2017 bisa zarginshi da aikata laifuka shida da suka hada da halatta kudaden haram da dai sauransu.

To Saidai wata daukaka kara da shugaban kamfanin NNPC din ya daukaka, kotu tayi fatali da wasu daga cikin tuhume tuhumen da ake mashi da suka hada da halarta kudin haram.

A hukuncin da kotun ta yanke, hakuncin da alkalin kotun ya yanke a jiya Alhamis, ya ce masu gabatar da kara sun gaza samar da abubuwan da ake bukata da za su sa a yanke wa Mr. Yakubu hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here