Kotu ta umarci a ci gaba da tsare Omoyele Sowore

Wata kotun majistire a Abuja ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare Omoyele Sowore, ɗan gwagwarmayar nan kuma tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya, a gidan gyara hali.
‘Yan sandan birnin Abuja sun gurfanar da mawallafin jaridar Sahara Reporters ɗin ne tare da wasu mutum huɗu a gaban kotu saboda zargin yin taro ba tare da izini ba da kuma uzura wa mutane.
Dukkanin mutanen sun musanta zargin da ake yi musu, kuma za a ci gaba da tsare su har zuwa gobe Talata domin sauraron ƙudirin neman beli.
An kama Sowore ne bayan ya jagoranci wata zanga-zanaga ranar Alhamis a Abuja.