Kotu ta tuɓe ƴan majalisar jihar Cross Rivers 20 da suka sauya sheƙa

Kotu

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori ƴan majalisar dokokin jihar Cross River guda 20 da suka sauya sheƙa.

Jam’iyyar PDP ce ta shigar da ƙarar ‘yan majalisar kan sauya sheka da suka yi zuwa jam’iyyar APC.

A ranar litinin ne kotun ta zartar da hukuncin, kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito.

Alƙalin kotun ya ce, ƴan majalisar su bar kujerunsu bayan sun yi watsi da jam’iyyar da ta ɗauki nauyinsu har suka samu muƙaman.

Ƴan majalisar dai na da damar ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin kotun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here