Kotu ta haramta wa Hamma Amadou takara Shugabancin Nijar
Daga Tukur Sani Kwasara
Kotun tsarin mulki a jamhuriyyar Nijar ta yi watsi da takarar madugun adawa na kasar Hamma Amadou.
A wata sanarwa da takaran to gaban maneman labarai a Yamai a ranar juma’a, kotun ta bayyana sunayen ‘yan takarar da suka cika dukkan sharuddan da dokokkin kasar suka shata.
Yan takara 30 ne sukayi nasara ketare siradi daga cikin yan takara 41 da takardun su suka jewa kotun.
Daga cikin su akwai dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya Bazoum Mohammed da yanzu haka wasu yan adawa suka shigar da kasar sa a kotu, suna kalubalanta takardarsa ta zama cikakken dan kasa.
Saidai 11 daga cikin yan takarar har da dan takarar jam’iyyar adawa ta Moden Lumana kuma madugun adawar kasar Hamma Amadou.
Matsalar safarar jarirai daga tarayyar Najeriya da wata kotu a Yamai ta kama Hamma Amadoun da laifin aikatawa ta kuma yanke masa hukuncin zama gidan yari na shekara daya ta zama Ummul’aba’isin rashin sa shi daga kotun tsarin mulki.
A tsarin mulkin Nijar rashin amincewa da takara ta Hamma Amadou da sauran yan takara goma 10 na nufin baza suje zabe ba, ta haka kuma jam’iyyun suma ba zasuje zaben shugaban kasa ba.
A Ranar 27 ga watan Disamba mai zuwa ne ake gudanar da zaben Shugaban kasar zagaye na farko da yan takara 30 zasu fafata.