Koto ta daure wata matsakaiciyar mata mai kimanin shekaru 38 a gidan yari daurin shekaru dari da biyu. Kotun ta samu matar mai suna Kiristina ne da laifin kwanciyar aure da dan shekaru 12 sannan kuma ta bashi tabar wiwi ya cake.

Kotun dake a jihar Nebraska a kasar Amurka, ta bayyana cewar sai matar tayi shekaru 64 a daure idan ta gyara halinta sannan za a dubua yuwuwar sassauta mata wannan hukunci.

Matar dai ta zakkewa yaron mai shekaru 12 a lokacin da ya shigo gidanta tare da ‘yarta mai shekaru 13. Matar ta baiwa yaron tabar wiwi ya sha ya kwale sannan ta dinga aikata masha’a da shi cikin dare

Daga
Scoop News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here