Kotu ta daure wani matashi a kurkuku saboda yayi rubutu kan Gwamna Badaru a Facebook
Babbar kotun Majastire dake zamanta a birnin Dutse na jihar Jigawa ta yankewa Sabiu Ibrahim Chamo hukuncin daurin wata shida a gidan kurkuku sakamakon kalaman bata suna da yayi ga Gwamna Badaru Abubakar.
Matashin dai ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar Gwamnan ya karbi kudin mutane da yawa dan ya basu takara daga karshe ya wofantar da su, zargin da matashin ya kasa karewa da hujja, a saboda haka kotu ta same shi da laifi.
Kotun ta daure matashin watanni shida a gifan kurkuku ko kuma zabin biyan tarar Naira dubu ashirin tare da Bulala ashirin ta je ka gyara halinka.
Mun Ciro daga shafin Daily Nigeria hausa