Mai Shari’a Aminu Garba Sifawa na Babbar Kotun Jihar Sakkwato da ke zaune a Sakkwato, a ranar Laraba 22 ga Satumba, 2021 ya yanke wa wani mai suna Aminu Mohammed Gobirawa, Daraktan Tsare -tsare, bincike da Kididdiga na Hukumar Ilimi ta Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu hukuncin daurin watanni shida saboda zamba cikin aminci.

Sokoto Tracker ta ruwaito cewa Kwamishinan Sakkwato na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ya gurfanar da Aminu a kan tuhuma guda ɗaya ta yaudara.

Gobirawa ya fara fuskantar tuhuma ne, cikin watan Mayun 2018, lokacin da ya tattara jimlar kudi N300,000 daga wasu mutane bisa dalilin cewar zai samar musu ayyukan yi cikin Hukumar Shige da Fice ta Najeriya.

Saidai daga karshe alkawarin samar da aikin ga mutanen ya ci tura.

Lokacin da aka karanta wa wanda ake tuhuma laifin, ya amsa laifinsa.

Dangane da laifin da ya aikata, lauyan masu gabatar da kara, Mela Gwani ya roki Kotu da ta hukunta wanda ake tuhuma daidai gwargwado.

Mai shari’a Sifawa ya yanke masa hukuncin daurin wata shida ko zabin biyan tarar N50,000 tare da daure na makwanni biyu a matsayin tsawatarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here