Advert
Home Sashen Hausa Ko kun sani......? Nasarorin Gwamnatin APC...!

Ko kun sani……? Nasarorin Gwamnatin APC…!

Ko kun sani……?

Nasarorin Gwamnatin APC…

 @Kokunsani.ng

Yana daga cikin Nasara da kawo ci gaba a jihar Katsina, Samar da Ofishin mai bawa Gwamnan katsina shawara akan Dabbobi da gandun Daji…wasu shekaru da suka shude mai girma Gwamna Aminu Bello Masari, ya shiga Dazuka inda rashin tsaro yafi kazamta a yankunan Katsina, ƙananan hukumomi goma sha daya, inda ya tattauna da munan yankin, domin samar da tsaro, da dauwammen zaman lafiya, inda suka sheda mashi, sufa Gwamnati basuma san ana yi, ba. Basu da Makarantar Boko basu da ta Islamiyya, basu da Asibiti Balle masallaci, ruwan sha, kuwa sai dai suji wai.

A dalilin haka Gwamnatin Katsina, ta sha alwashin aiwatar masu da wadannan ababen na more rayuwa. Sana kuma ta ƙirƙiro Ofishi na Musamman da zai bawa Gwamnan Katsina shawara akan Dabbobi da gandun Daji, inda aka samar da ofishin wanda masani Dakta Lawal Usman Bagiwa ke shugabanta, wanda aka gina akan abu uku. Na ɗaya don samar da dauwammen zaman lafiya tsakanin Makiyaya da Manoma, na biyu don kara Inganta da samar da wani yanayi mai kyau ga dabbobin, na gida da na Jeji, da kuma gudanar da tsarin kiwonsu daidai da zamani, na uku don don kare Cututtuka da ke yaɗuwa tsakanin Mutane da dabbobin.

Haka kuma Ofishin yana da ɓangarori biyar da ya maida kai akansu, na farko ɓangaren kula da dabbobin kansu, Nomansu da Ingantasu (Livestock) na biyu bangaren kula da lafiyar Dabbobi (Vatinarry) na uku bangaren kula da kare Cututtuka daga Dabbobi zuwa mutane, da kuma samar masu da yanayin tsafta, sai na hudu da na biyar sune, bangaren harkokin Mulki da na kuɗi.

Acikin shekaru biyu da samar da wannan Ofis da zai taimaki Al’uma da rayuwarsu… Gwamnatin APC a ƙarƙashin wannan ofishi tayi Nasarar, yin Allurar rigakafi na cututtuka ga Dabbobi irin su ciwon Huhu, murar tsuntsaye,da cutar Haukan kare. Inda tayima Manyan Dabbobi kamar su raƙuma da Shanu, guda dubu ɗari tara, rigakafi a faɗin jihar katsina, sai kuma ƙananan Dabbobi Irin su Tunkiya awaki, da makamantan su, su kuma an samu nasarar yiwa guda dubu ɗari takwas da tamanin Allurar rigakafin, kamar yanda Ofishin Dakta Bagiwa ya sanar… Wannan ba karamar nasara bace ga Gwamnatin APC da Al’umar jihar Katsina… www.kokunsani.ng

 

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE BUHARI ADMINISTRATION SUPPORTS THE LAGOS STATE RAILWAY PROJECT!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/232549375628254/

Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Bauchi

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar. Rahotanni sun baiyana cewa shi dai Misau yaron Ministan...

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths editorDecember 5, 2021 4:50 Pm Francis Sardauna in Katsina Ahead of the 2023 general election, the...

‘Yan Bindiga Sun Tsananta Kai Hare-hare Akan Hanyar Gusau Zuwa Shinkafi

Daga Dauda Umar Januhu 'Yan Bindiga a jihar Zamfara suna cigaba da kai zafafan hare-hare tare da sace mutane akan babbar hanyar da ta tashi...

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano…

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano Jami'an Ƴan sandan Farin Kaya, DSS sun kama Janar Idris Dambazau, Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayan Kaya...