Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alh Mannir Yakubu ya danganta kalubalen tsaro da ake fuskanta a ƙasar nan da rashin kulawa da iyakoki da gwamnatoci ke nunawa.

Alhaji Mannir Yakubu ya baiyana haka a lokacin da yake jagorantar taron masu ruwa da tsaki akan batun iyakar Katsina da Zamfara.

Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara wanda ya samu wakilcin babban sakataren ofishin sa Alhaji Mainasara Shehu Bakura da babban daraktan hukumar shata iyakokin ƙasa Adamu Adaji da dai sauransu.

Alhaji Mannir Yakubu ya nuna bukatar da ke da akwai na tattaunawa da masu ruwa da tsaki wajen shawo kan matsalar tsaro a iyakokin jahohin guda biyu.

A jawabinsa mataimakin Gwamnan jihar Zamfara wanda ya samu wakilcin babban sakataren ofishin sa Alhaji Mainasara Shehu Bakura ya jaddada bukatar da ke akwai na tattaunawa akan iyakokin jahohin don shawo kan matsalar tsaro da ke fuskantar yankunan jahohin.

Ya kuma yabama kokarin hukumar shata iyakokin ƙasa bisa kokarin ta na tabbatar da iyakokin jahohin ƙasar nan.

Babban daraktan Hukumar shata iyakokin jahohin ƙasar nan Adamu Adaji ya nuna godiyar sa ga Gwamnatocin jahohin guda biyu da Sarakunan yankin bisa rawar da suka taka wajen bayar da dama ga jami’an hukumar don gudanar da ayyukan su.

Daga bisani an fitar da takardar bayan taro da ke kunshe da shawarwari da kuma yarjejeniyar da aka cimma wa a lokacin taron takardar dake dauke da sanya hannun duka bangarorin.

Muhammad Barmo Hadimi Na Musamman Ga Mataimakin Gwamna Akan Sababbin Kafafen Sadarwa Da Yada Labarai ( New Media ) 6/10/2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here