Advert
Home Sashen Hausa Kisan Sayyidina Hussain:- SHI NE MAFI MUNIN ABINDA BA A TAƁA YI...

Kisan Sayyidina Hussain:- SHI NE MAFI MUNIN ABINDA BA A TAƁA YI BA A TARIHI.  -Sheikh Aminu Daurawa Kano

Kisan Sayyidina Hussain:- SHI NE MAFI MUNIN ABINDA BA A TAƁA YI BA A TARIHI.  -Sheikh Aminu Daurawa Kano

“To Alhamdulillahi kamar yadda aka shina wannan abu ya faru ne ranar 10 ga watan Almuharram shekara ta 61 bayan hijira wanda yayi dai-dai da 10 ga watan Oktoba shekara ta 680 Miladiyya a Karbala, wanda Karbala kuma tana cikin Iraƙi.

To na farko dai rigingimu ne na siyasa shi Sayyidina Hussaini jikan Manzon Allah ne (S) ɗan gidan Fatima da Aliyu, kuma shi ne na biyu a cikin ’ya’yan Fatima da Aliyu bayan Hassan. To bayan an yi wa shi Yazidu mubayi’a shi Hussaini yana cikin waɗanda basu gamsu da Yazidu ya zama shugaban Musulmi ba amma kuma bai tada wata ƙura ba bai yi wata magana ba kuma bai ɗauki wani mataki ko wane iri ba, dan haka ya koma Madina ya yi zamansa.

To da abubuwa suka yi zafi suka riƙa aika masa wasiƙu cewa ba su gamsu da yadda ake gudanar da mulki ba musamman a yankinsu na iraƙi suna son ya taso domin ya zo ya taimaka masu su fita daga cikin wannan ƙangi ta hanyar su naɗashi a matsayin shugaba. Da ya ƙi yarda amma wasiƙu su kai ta zuwa ta fuskoki daban-daban har ya gamsu ya tura ɗan’uwansa ko ɗan-ɗan ɗan’uwansa ya je ya bincika masa (Aƙeelu), ya nuna masa cewa lallai akwai bayani da ke nuna cewa da waɗannan Mutane da gaske su ke zasu taimaka masa, kuma suna cikin halin ƙaƙa-ni-kayi suna buƙatar ya zo domin su yi masa mubayi’a a matsayinsa na shugaba.

Duk waɗannan abubuwa da suka faru su basu fahimci cewa akwai rigingimu na siyasa mai ƙarfi da za a iya amfani da makamai ba dan haka ya rubuta wa Hussaini wasiƙa cewa; ya gamsu mutanan nan da su ke ta rubuta masa wasiƙa dodo-dodo su ke so ya taso daga inda ya ke ya zo nan suyi masa Mubayi’a ya shugabancesu da gaske su ke kuma ya ga su na da mutane da yawa in ma wata rigima ta taso a shirye su ke su bashi kariya ko da hakan zai iya salwantar da rayuwarsu, dan haka ya gamsu ya ɗebo iyalansa gaba ɗaya ya taho.

To daga baya shi wakilin nasa a can sai ya fahimci abin akwai yaudara, waɗanda suka nemi ya taho ɗin ba da gaske su ke ba wato shigo-shigo ba zurfi ne ba su da karfin tare masa rigima idan ta taso ba zasu iya taimaka masa idan yaƙi ya tashi ba. Ya aika masa wasiƙa ta biyu, wasiƙa ta biyun ba ta iso zuwa gareshi ba ko ba ta kai gareshi ba har ya riga ya shigo gurin. Sai da ya shigo sai su kuma su nan suka samu labarin Hussaini ya taso.

Saboda haka suka fitar da Sojojinsu domin su tare shi (su Gwamnatin Yazidu kenan) wanda gwamnansu da ke wannan guri wanda ya ke a kufa ɗin wanda shi ne ya jagoranci wannan wadanda suka fito. To tattaunawa ta kai dai Shi Hussaini ya nemi ayi masa ɗayan 4: na farko ya ce; a bashi dama ya tafi can Siriya ko kuma mu ce wato sham, inda shugaba, kamar nan ne fadar shi Yazidu, shugaban ƙasa na Musulmi na lokacin, ya tafi ya same shi su tattauna shi da shi. Su ka ce basu yarda da wannan ba. Na biyu ya ce su bashi dama ya koma inda ya fito ma’ana ya koma Makka ko ya koma madina tare da iyalansa, wannan ma su ka ce ba su yarda ba. Ya ce to su bashi dama ta ukku ya tafi can wata ƙasa ya kama wa’azi da karantarwa ya fita daga cikin harkar Mulki da harkar wannan siyasa wadda ga abinda ta zama, nan ma suka ce basu yarda ba, ya ce to mi su ke so? Suka ce sai dai yayi saranda ya miƙa wuya a matsayin an ci shi da yaƙi da shi da mutanansa. Sa’annan ne ya ce shi kuma ba zai ƙasƙanta kanshi ba, ba kuma zai aminta ba.

To daga nan ne harkar yaƙi ya ta ɓarke a tsakani wanda shi bai da mutane da yawa su kuma waɗancan mutane da suka yi masa alƙawari duk sun gudu su ma daga cikin waɗanda su ka zo su yaƙe shi suna cikin waɗanda suka dinga tura masa wakilai wasu ma duk ya gane fuskokinsu cewa ba ku kuka gayyato ni ba? Ba kuka rubuta mani wasiƙa ba? Ba kuka ce in taso zaku tallafa man, zaku bani goyon baya ba? Ya gaggane fuskar wasu (akwai munfunci a ciki.

Daga nan ne suka juya masa baya har ya kai ga abinda ya faru na ta’addanci na zubar da jini kuma mafi munin abinda ba a taɓa yi ba a tarihi ba kuma ba ƙara yin irin shi a tarihi ba, yayin da aka kashe iyalan gidan Manzon Allah (S) dan da yawa sojojinsa duk jinin Manzon Allah ne. To a nan ne aka yi wannan kisa mai yawa inda aka kashe shi (Hussain) aka kashe da yawan jikokin gidan Manzon Allah (S) a wannan guri.

Bayan an gama yaƙin akwai Aliyu Binil Hussain ɗansa kenan lokacin yana ɗan karami sai kuma ya ga mutanan gari sun fito sun ji labarin ai an kashe Hussaini gashi ma har an kama Matansa da ƙananan yara a matsayin fursunonin yaƙi za a tafi da su zuwa Sham. Sai ya ke ce masu kuna mana kuka ba ku kuka gayyato mu ba kuma kuka je kuka ɓuya a gidajenku kuka bari sai da aka kashemu sannan zaku fito kuna dukan kanku kuna kuka? Miye amfanin wannan kukan naku?

Da farko shi dama akwai ita Shi’a kashi biyu ce, akwai Shi’a ta soyayya da ƙauna kana son Mutum sai a kiraka Shi’arsa kamar mai goyon bayansa kenan. Akwai kuma Shi’a ta aƙida da Ibada da wasu kuma ayyukan ibada to ita wannan bayan kashe Hussaini ta fara waccan ita Shi’a ta goyon bayan gidan Annabi (S) da san iyalansa da fifitasu akan kowwane gida dama akwaita wannan a lokacin cewa ko kuma ita kamar halitta ce ta mutum ɗabi’a ce in dai akwai mutane biyu ko Ukku sai kaji kafi son wani.

Eh dama in ka kula ai a ranar 10 ga watan Almuharram ranar Ashura a ranar abin ya faru, ranar ne su Shi’a suka ƙirƙiro a ranar a riƙa sa baƙaƙen kaya kuma a dinga nuna jimami a dunga zaman makoki na wannan abu da ya faru daga baya ne zaka ga wasu har su kan dinga amfani da ƙarafuna wasu kuma na amfani da wuƙaƙe wasu kaga sun zuba garwashin wuta suna takawa suna bi ta kai, wasu kaga sun sa lauje haka mai kamar wuƙa suna yankawa a bayansu har kaga jini yana kwarara, wanda wannan ma su Shi’a ɗin sun yi fatawa cewa wannan abin ba adduni bane”.

Wannan Wata Fira ce da gidan Redion Jamus yayi da Malamin kan abinda ya faru a ranar Ashura na Kisan Imam Hussain (A.S).

_Bin Yaqoub Katsina✍🏾

11-1-1443(20-9

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: