Advert
Home Sashen Hausa Kisan Filato: Rundunar Ta Yi Allah Wadai Da Kiran A Sauke Janar...

Kisan Filato: Rundunar Ta Yi Allah Wadai Da Kiran A Sauke Janar Ibrahim Ali

Rundunar Sojin Nigeria da Babbar Murya tayi Allah wadai da Kiran a sauke Babban Kwamanda na Rundunar ta 3 na Soji Manjo-Janar Ibrahim Ali, akan zubar da jinane a Jahar Filato

Ali ya kasance Kwamanda ne na Musamman na operation Save Haven dake kula da Jahar Filato da wasu sassan Jahar Bauchi da Kaduna.

Majiyar Jaridar Dimokradiyya ta ruwaito cewa, a halin yanzu Janar Ali baya jindadin zama da Al’ummar Filato, Wanda suke cewa ya kasance yana goyon bayan wani bangare na Al’ummar Jahar.

Mutanen Jahar sun Kuma cigaba da kira ga Babban Hafsan Sojin Kasa Laftanar-Janar Farouk Yahaya daya kawo wanda zai gaje shi.

Hadaddiyar Kungiyar kabilun Filato tabi sahu wajen yin Kiran, inda ta nuna rashin jindadi akan kashe-kashe a Bassa, da Jos ta Arewa, da Miango, da Riyom, da Mangu, da Rukuba, da Yelwa Zangam da sauran su.

An dai kalubanci janar Ali da rashin iya aiki, wanda yayi sanadiyyar Mutuwar mutane da rasa dukiyoyi, a inda yake kula dashi.

Irin wannan Kiran dai Kungiyar Kiristoci ta Kasa reshen Majami’ar ECWA/TEKAN sun taba yinshi.

Tunda Farko, wani bangare na mutanen Filato sunce Ali na kokarin shafe Yan asalin Garin, zargin da Soji suka karyata.

A cikin sanarwar da Rundunar Soji ta fitar a cikin hutun makon nan, Rundunar soji tace maganganu da akeyi ga GOC, abune da akeyi domin kawo tsaiko a kokarin shi na maido da zaman lafiya.

Mataimakin Daraktan Yada Labaru na Rundunar Soji na bariki na 3 Major Eli Lazarus ta bayyana haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: