… An kama kwayar Heroin a filin jirgi, an cafke matar da ta saka hodar iblis a abinci ta kawo wa saurayin ta wanda yake garkame a ofishin NDLEA

Yunƙurin safarar miliyoyin miyagun ƙwayoyi a jihar Lagos da ma sauran sassan ƙasar nan a yayin bukukuwan ƙarshen shekara ya gamu da cikas, inda hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA, ta kama kafson Tramdol kimanin 8,381,600 tare da kwalaben Codeine guda 56,782 da ma sauran sinadarai a manyan sumame da hukumar ta kai a birnin Legas.

Kafin bukin Kirsimeti, shugaban hukumar ta NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya ya bada umurnin saka ido a wasu kebantattun wurare a cikin yankin Alaba Rago na jihar Lagos. Biyo bayan hakan, jami’an hukumar sun kai sumame a ranar 23 ga watan Disamba, inda suka yi nasarar kama ƙasurgumin dillalin ƙwaya, Ezekiel Ibe dauke da sama da tan biyar na ƙwayoyin tramadol a gidan ajiyar sa. Ƙwayoyin da aka kama a wurin sa sun hada da Tramadol guda 7,991,600, da Kafso guda 390, 000 wadanda duka nauyin su ya kau kilograms 5,468.

A wani suname da hukumar ta kai a ranan litinin, 20 ga watan satumba a wani wuri da ya jima ana sanya ido a kai, a garin Alaba dake jihar Lagos inda aka kama wani mai suna Surajo Mohammed dauke da wiwi mai nauyin Kilogram 941.14, yayin da kuna aka bankaɗo Kwalaben Codeine guda 56,782 a wani gidan ajiya mallakar dillalin ƙwayoyi.

A daya ɓangaren kuma, jami’an hukumar sunyi nasarar kama mace mai shekaru 22, Amaka Ogonachukwu bisa laifin shigo da kullin hodar iblis ɓoye a cikin dafaffen shinkafa zata kaiwa saurayinta mai suna Monday Imagbebenikaro, nai shekaru 40, wanda yake kulle a ofishin NDLEA na jihar Edo. Monday ya shiga hannun hukumar ne lokacin da aka kama shi a kan hanyar filin jirgi a ƙaramar hukumar Oredo bisa laifin safarar hodar iblis, wiwi da kuma Danabel.

Kazalika an kama wani fasinjan jirgin Turkiyya mai suna Ovire Cyril dauke da kullin heroin guda 114 wanda nauyin su yakai Kilogram 1.80 yayin da ake binciken fasinjoji a filin jirgi na Murtala Muhammad dake birnin Ikko, Legas. Cyril ya ɓoye ƙwayoyin ne a cikin aljifan wando guda huɗu, sannan ya saka su a cikin jakar daukan suit. A yayin da ake binciken sa ha bayyana cewa ƙuncin rayuwa ne ya sanya shi faɗawa cikin wannan yanayi, inda yace an yi masa alƙawarin kuɗi kimanin €5,000.00 idan yayi nasarar safarar ƙwayoyin zuwa ƙasar Italiya.

Haka kuma an kama wani fasinjan jirgi mai suna Osakue Evbuomwan a kan hanyar sa ta zuwa Milan a ƙasar Italiya, dauke da Kilogram 1.55 na Tramdol ɓoye a cikin jakkar Ghana must go.

Shugaban hukumar, Janar Buba Marwa mai ritaya ya jinjinawa kwamandoji, da sauran jami’an hukumar na jihohin Lagos, Edo da MMIA saboda rashin ƙasa a guiwa a yayin bukukuwan ƙarshen shekara. Marwa ya kuma tabbatar musu da cewa shugabancin sa zata cigaba da sakayya ga wadanda suka nuna hazaƙa a bakin aikin su, inda ya nemi su cigaba da ƙokari fiye da yanda suke yi a baya.

Mahmud Isa Yola
Hedikwatar NDLEA, Abuja
Lahadi, 26 Disamba, 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here