Gwamnatin tarayya ta sanar da fara jigilar ‘yan Najeriya ta jirgin kasa kyauta tun daga ranar 24 ga watan Disamba har zuwa 4 ga watan Janairu na shekarar 2022.

Manajan darakta na hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya (NRC), Fidet Okhiria, ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a.

Ya ce: “Shawarar da a ka yanke tare da hadin gwiwar ma’aikatar sufuri, ita ce ta saukaka zirga-zirgar ‘yan kasa a lokacin bikin Kirsimitei na yuletide.

Ya nanata kudirin gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji da jiragen kasa a wannan lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here