Kin amincewa da ‘Yan sandan Jihohi: Buhari yai mun dai dai – Inji Shehu Sani

Akwai fargabar cewa samar da ‘yan sandan jihohi zai fi haifar fa illa fiye da alheri

Wannan shi ne matsayin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu

Shi ma dai tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya ce wasu gwamnonin za su yi amfani da ‘yan sandan jihar a matsayin makami wajen kai wa masu zagin su hari.

Tsohon dan majalisar dattawan Kaduna, Sanata Shehu Sani, ya ce yana goyon bayan kin amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na samar da ‘yan sandan jihohi a fadin Najeriya.

Dan jam’iyyar PDP kuma jigo a jam’iyyar ya ce idan har aka amince da hakan, gwamnonin jihohin da suke kallon kansu a matsayin makura za su yi amfani da abin da bai dace ba.

Sani ta shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, ya kai ga yin ikirarin cewa irin wadannan gwamnonin za su ga cewa an dauki ‘yan barandan siyasa a cikin rundunar domin warware masu adawa da su.

Ya ce rundunar ‘yan sandan jihar za ta kasance tamkar hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha (SIECOM).

Hoto 📸 Legit.ng

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here