Yadda ƴan ta’adda su ka tafi da uwa kuma su ka bar ƴarta jaririya ita kaɗai a jeji

Ƴan ta’adda masu fashin daji sun yin garkuwa da matafiya da dama, har da wata uwa mai shayarwa a Sheme, kan titin Katsina zuwa Gusau.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawiato cewa harin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 8 na dare yayin da maharan su ka kwantar da ɗaruruwan matafiya a hanyar.

Hafizu Aliyu na cikin waɗanda harin ya rutsa da su amma ya samu damar kuɓuta ya kuma ɗauki jaririyar.

Aliyu ya ce a lokacin da ƴan ta’addan su ka yi awon gaba da mutane, uwar jaririyar ta yi ta magiya da su ƙyale ta ta tafi da ƴarta amma su ka ƙi yarda da roƙon ta, inda su ka tafi da ita su ka bar jaririyar ita kaɗai a jeji.

“Mu na cikin tafiya a kan titin Katsina zuwa Gusau, a daidai tsakanin Sheme da Ƴankara sai a ke ce mana ƴan fashin daji su na nan gaba, sai mu ka tsaya har tsawon mintuna 40 mu na jiran sojoji.

“Da Sojojin su ka zo, sai su ka ce mana kar mu matso gaba su za su tafi su yaƙi ƴan ta’addan gudun kada abin ya shafi ƴan ba ruwa na. Bayan kamar mintuna 30 sai su ka dawo su ka yi mana jagora. Sai motocin sojojin su ka shiga gaban mu amma da tazara a tsakanin sauran motocin da ke bin su.

“Da su ka ji ƙarar harbin ƴan ta’addan ya fi ƙarfin nasu, sai sojojin su ka juyo su ka ce mana muma mu. To a kwai sama da motoci ɗari, ba zai yiwu duka a juya ta sauki ba, kawai sai dai kowa ya sauka ya yi ta kansa.

“Ina dirowa daga motar sai na ji ciwo a ƙafa. Da na ji ba zan iya gudu ba kawai sai na kwanta a ƙarƙashin wata mota. Da ƴan ta’addan su ka karaso, sai su ka bi waɗanda su ke gudu, waɗanda kuma su ka ƙasa gudu, sai su ka kaɗa su cikin jeji.

“Ina kwance a ƙarƙashin motar na ɗauke wuta, sai na ji uwar tana ‘ƴa ta, ƴa ta’, amma ƴan ta’addan su ka ƙi sauraren ta su ka tafi da ita sannan su ka bar yarinyar ita kaɗai a jeji.

“Bayan kamar mintuna 30 ina ƙarƙashin mota, da na ji alamun ƙafa ta ɗauke ƴan ta’addan sun tafi, sai na fito na nemi inda jaririyar take. Wajen ya yi tsit ba ƙarar komai sai kukan yarinyar.

“Da ga nan na ɗauke ta na yi ta tafiya, ban san ina nake dosa ba. Sai da asuba na karaso wani ƙauye mai suna Kuchere, in da mutanen garin su ka sauke ni su ka bamu abinci. Har sai da mura ta kama yarinyar sabo da iskar da ta shiga, shine sai mutanen su ka bata maganin gargajiya.

“Ga yarinyar ba ta iya magana sai dai kuka. Gashi ba mu san sunan ta ba, ba mu san ma wacece mahaifiyarta ba.

“Bayan na bar ta a hannun dagacin garin, sai na fara ƙoƙarin dawowa gida Zariya,” Aliyu ya shaidawa DAILY NIGERIAN.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here