Advert
Home Sashen Hausa Katsina: Masari Ya Kafa Kwamitin Binciko Marayu Da Zawarawa

Katsina: Masari Ya Kafa Kwamitin Binciko Marayu Da Zawarawa

Katsina: Masari Ya Kafa Kwamitin Binciko Marayu Da Zawarawa

Majalisar zartaswa ta jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kafa wani kwamiti na musamman, domin zakulo yawan marayun da suka rasa iyayen su da kuma zawarawa da suka rasa mazajen su, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a kananan hukumomi goma sha daya da suke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina.

Kwamishinan yada labarai na jihar Katsina da harkokin cikin gida, Alhaji Abdulkarim Yahaya Sirika ya bayyanawa manema labarai hakan, bayan kammala zaman majalisar zartaswa da gwamna Masari ya jagoranta a ranar laraba.

Abdulkarim Yahaya Sirika ya kara da cewa an zabo mutane ashirin, wanda aka zabo daga fannoni daban-daban, wanda mataimakin gwamna, Alhaji Mannir Yakubu zai jagoranta. Aikin kwamitin shi ne ya gano hakikanin yawan zawarawa da marayun da suka rasa iyayensu, domin duba yadda gwamnati za ta taimaka masu.

Kananan hukumomi da ke fama da wannan matsalar ta rashin tsaron sun hada Batsari da Dutsinma da Faskari da Sabuwa da Dandume da Safana da Jibia da Danmusa da Kankara da kuma Kurfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Northern Group defends suspended NPA MD, accuses Amaechi of Witch-hunt

Northern Group defends suspended NPA MD, accuses Amaechi of Witch-hunt By Saxone Akhaine, Kaduna 15 May 2021   |   4:12 am   Amaechi Arewa Youths under the umbrella of...

Mata ayi hattara: Wani mazanbaci yana amfani da social media wajen yiwa mata fyaɗe kuma ya kashesu

TURKASHI: Dubun wani matashi ta cika da ya kware wajen shigar attajirai a social media yana gayyatar yan mata wajensa da sunan zai basu...

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Dauke Da Bundigu Da Harsashai A Jihar Zamfara

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Dauke Da Bundigu Da Harsashai A Jihar Zamfara Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Maigirma Gwamna Matawalle ta yi nasarar...

Rikicin Isra’ila da Falasɗinawa: Su wane ne Larabawan Isra’ila?

Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa: Su wane ne Larabawan Isra'ila? 14 Mayu 2021 Wannan makon ya kasance mai cike da rikici a yankunan Isra'ila da Falasɗin. Bayan shafe...
%d bloggers like this: